DSS ta kama mutum biyu a Kano kan zargin tayar da rikici

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ce ta kama wasu mutane biyu da take zargi da tunzura mutane domin tayar da hankali a jihar Kano gabanin zaɓen gwamna da na ‘yan majalisun jiha da za a yi a ranar Asabar. Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter hukumar ta DSS ta ce mutanen sun naɗi hoton bidiyo ne da suke bayanan tunzura jama’a a cikinsu, sannan suka riƙa wallafa shi a shafukan sada zumunta. Ta kuma wallafa sunayen Sharu Abubakar Taɓule mai shekara 37 a duniya, da kuma Isma’il Iliyasu Mnagu mai shekara 51 a matsayin waɗanda ta kama. “Cikin waɗannan saƙonnin masu haɗari, sun nuna jam’iyyar siyasar da suke goyon baya kuma suka yi kira ga magoya bayansu su kai wa abokan hamayyarsu hari duk inda suka gansu. “Waɗanda ake zargin sun yi kira da a kai wa jami’an tsaro hari yayin zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi da za a yi a ranar Asabar. “Wata jam’iyyar siyasa a Kano na barazanar shirya zanga-zanga a sakamakon shirin kai ...