Search This Blog

Saturday, 31 December 2022

Sojojin haya sun kama jirgi maƙare da fetur na sata a Neja-Delta



Kamfanonin tsaro biyu da Najeriya ta bai wa kwangilar tsaron bututan man fetur sun kama jiragen ruwa da mota maƙare da man da hukumomi suka ce na sata ne a yankin Neja-Delta da ke kudancin ƙasar.

Wata sanarwa da kamfanin mai na Najeriya, NNPC Limited, ya fitar a yau Asabar ta tabbatar mutum huɗu aka kama yayin samamen.

Kamfanin ya samu rahoton sirri game da ayyukan mutanen tun a ranar 22 ga watan Disamba.

Dakarun tsaro sun isa wurin kuma suka tarar da su suna jigilar man ta ɓarauniyar hanya tare da tace gas a wata matata da ke Agge.

Tuni hukumomi suka ƙona jirgin da kayan da yake ɗauke da shi.

Fetur

A tsakiyar shekarar 2022 ne gwamnatin Najeriya ta ƙulla yarjejeniya da kamfanonin Tantita Security Services da zimmar daƙile ayyukan ɓarayi da kuma masu fasa bututan mai a yankin na Neja-Delta.

Satar mai na jawo wa Najeriya asarar biliyoyin kuɗin shiga kuma ya sa ba ta iya haƙowa da fitar da ganga miliyan 1.8 da ƙungiyar Opec ta masu arzikin man fetur ta ƙayyade mata a kowace rana.

Friday, 30 December 2022

Bidiyo: Gasar sukuwar Dawaki ta Premier ta Birnin Kebbi. Rana ta daya zagaye na 2


 

Bidiyo : Gasar sukuwar Dawaki ta Premier Birnin Kebbi. Rana ta daya zagaye na 3


 

Thursday, 29 December 2022

Fitaccen dan kwallon duniya, Pele ya mutu

 



Fitaccen ɗan ƙwallon nan na duniya ɗan ƙsar Brazil, Pele ya rasu yana da shekara 82.

Pele ya rasu ne a ranar Alhamis 29 ga watan Disamban 2022 bayan ya sha fama da rashin lafiya.

A kwanakin baya an yi ta yaɗa labarin ƙarya na rasuwarsa.

Ya rasu ne sakamakon cutar kansar ƙaba da kuma cutar ƙoda

Ana ganin Pele shi ne ɗan ƙwallon da ba a taɓa samun irin sa ba a duniya, kuma sau uku yana cin gasar kofin duniya wa ƙasarsa Brazil.

Ya ci kofin duniya a shekarun 1958 da 1962 da kuma 1970.

A shekarar 2000 ne kuma hukumar ƙwallon ƙafar duniya FIFA, ta ayyana shi a matsayin ɗan ƙwallon ƙarni.

Shi ne ɗan ƙwallon da ya kafa tarihin zura ƙwallaye 1,281 a raga a cikin wasanni 1,363 cikin shekara 21 da ya yi yana buga tamaula.

Cikin waɗannan har da ƙwallo 77 da ya ci wa ƙasarsa cikin wasanni 92 da ya buga wa Brazil ɗin.

An yi wa Pele tiyata a kan yanke masa kansa a hanjinsa a watan Satumban 2021 a Asibitin Albert Einstein da ke Sao Paulo.

An sake kwantar da shi a asibiti a watan Nuwamban 2022.

Ƴarsa Kely Nascimento ta yi ta sanar da masoya halin da mahaifinta ke ciki a shafukan sada zumunta daga asibitin da yake jinya.

A ranar Alhamis ɗin ta wallafa wani hoto da ke nuna hannayen iyalan Pelen a kan jikinsa a asibiti inda ta rubuta: "Muna maka godiya kan duk abin da ka yi mana. Muna matuƙar ƙaunarka. Allah Ya ji ƙanka.

Buhari Zai Sayo Motocin Sulke 400 Don Tsaron Su Abuja



Shugaba Buhari ya amince da sayo motocin sulke guda 400 don amfani da su wajen tabbatar da tsaro a babban birnin tarayya da jihohin Nasarawa da kuma Neja.

Sabon Kwamandan Rundunar Tsar Birgediya, Manjo-Janar Mohammed Usman ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a jawabin godiyarsa a bikin nada masa anininsa bayan karin girma da ya samu.

Shugaban kasa tare da Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Faruk Yahaya da uwargidan kwamandan, Dokta Rekiya Usman, ne suka nada masa aninin.

Jim kadan bayan kammala bikin a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, shugaban kasa ya bayyana shi a matsayin fitaccen jami’in da yake yi wa kasa hidima.

Buhari, a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Garba Shehu ya fitar, ya yaba wa iyalan kwamandan bisa hakurin da suka yi na jure kalubalen da ya fuskanta wajen gudanar da aikinsa.

A nasa jawabin, Manjo-Janar Usman, ya gode wa shugaban kasa bisa irin gagarumin goyon bayan da ya bai wa Rundunar Sojin Najeriya, inda ya bayar da umarnin sayo motocin sulke guda 400.

A cewarsa, sun isa su tabbatar da tsaron yankin babban birnin tarayya, Nasarawa da sassan Jihar Neja.Ya bayyana farin cikinsa kan karin girma da aka yi masa, wanda ya ce  zai kara zaburar da shi wajen yin abin da ya dace game da nauyin da ya rataya a wuyansa.

(AMINIYA)


Wednesday, 28 December 2022

Ka da ka shekara goma da mata daya - Sheikh Daurawa

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce shawarci maza cewa ka da su kuskura su shekara 10 da mace daya matukar suna da burin kara aure.

Sheikh Daurawa, ya bayyana haka ne a zantawarsa da gidan rediyon Freedom da ke Kano haka ne, inda ya ce idan namiji ya kai wannan shekarun da mace daya, lokaci ya kure masa.

“Kada ka wuce shekara 10 idan za ka kara aure ba ka kara ba. Idan ka wuce shekara 10 akalla kana da ‘ya ‘yar shekara takwas ko tara.

“Da zarar ’yarka ta kai shekara 15 ba ka kara aure ba, to wacce zaka auro da wuya ta wuce shekara 20. Za ka ga tsakaninsu da ’yarka bai wuce ’yan tazarar shekaru ba.

“Saboda haka matarka ta samu abokiyar rigima. Akwai wadda za ta iya tura ’yarta ta samu amarya su rika rigima ko ta yi ta dukan amaryar saboda ta fi karfinta.

“…Saboda haka wanda zai yi aure ya shirya da wuri, kuma kada duk dadin miyar mace ka ce ba za ka kara aure ba,” in ji Shehun malamin.

Karin aure ko yi wa uwar gida kishiya na tayar da kura a lokuta da dama, lamarin da ke haifar da mummunan kishi a tsakanin kishiyoyin.

A wasu lokuta ma ana rasa zaman lafiya a gidan, wanda hakan yakan kai ga yin saki don samun kwanciyar hankali.

Tuesday, 27 December 2022

Gasar sukuwar Dawaki ta Birnin Kebbi ta 2022. Rana ta daya zagaye na biyu

Almajiran Abduljabbar Kabara sun ce zasu daukaka kara

 


Almajiran Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da Kotun Musulunci ta yanke wa hukuncin rataya kan laifin batanci ga Manzon Allah (SAW) suna shirin daukaka kara.

Almajiran fitaccen malamin mazaunin Kano, karkashin inuwar A’shabul Kahfi Warraqeem, Reshen Jihar Bauchi, sun yi zargin siyasa a hukuncin da aka yanke masa, saboda a cewarsu, malamnin nasu ya caccaki Gwamnan Jihar Kano, kan zargin almundahana.

“Ba mu gamsu da hukuncin ba saboda muna zargin akwai hannun Gwamnan Jihar Kano da wasu malamai da suka dade suna zaman doya da manja da shi (Abduljabbar), wadanda suka yi masa kagen yin batanci domin su kawar da shi daga doron kasa ta hanyar amfani da karfin kotu,” in ji mai magana da yawunsu, Abdullahi Musa a Bauchi.

Ya shaida wa manema labarai cewa, “Zargin batancin ba komai ba ne illa neman goga masa kashin kaji daga magauta, ciki har da Ganduje da wasu malamai da ke ganin daukakar da Abduljabbar ke samu a matsayin baraza a gare su.“Shi ya sa suka jefe shi da yin batanci domin su ja masa bakin jini saboda su samu dalilin kawar da shi.

“Saboda haka mun yanke shawarar zuwa kotu ta gaba mu nemi ta soke wannan mugun hukuncin, tare da tabbatar masa da ’yancinsa, musamman na yin addini da bayyana ra’ayi kamar yadda kunin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.

“Muna rokon Hukumar Kare ’Yancin Dan Adam ta Kasa, kungiyar Amnesty International, da sauran kungiyoyin kare hakkin dan Adam na cikin gida da na kasa da kasa, da kuma lauyoyin kare hakkin dan Adam irin su Femi Falana, da mai rajin kare hakkin dan Adam, Ahmad Isa — Ordinary President, da sauransu, da su fito su yaki wannan zalunci da taron dangi da aka yi wa jagoranmu na addini, Sheikh Abduljabbar, ta hanyar sama mishi agajin shari’a,” in ji Abdullahi Musa.

Ya yi zargin hadin bakin Gwamnatin Jihar Kano da wasu malaman da ba sa shiri da Abduljabbar wajen hallaka shi a kan laifin da bai amsa ba.

“Mun lura cewa wadansu daga cikin wadanda suka yi taron dangi domin kawar da Abduljabbar, su ke aikata batanci a karatuttukansu, ba tare da wani tarnaki ba.”

(AMINIYA)

Na Daina Jin Dadin Rayuwa, Burina In Cika Da Imani Kawai – Aminu Dantata

 


Hamshakin  attajirin nan na Jihar Kano, Aminu Alhassan Dantata, ya ce daina jin dadin rayuwa, kuma ba shi da wani buri sama da cikawa da imani.

Attajirin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Mataimakin Dan Takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC, Kashim Shettima.

Ya ce ton tasowarsa, ya samu damar haduwa da mutane da dama, kuma ya kulla abota da jama’a a duka jihohin kasar nan.

Sai dai, ya ce a halin yanzu da walan gaske ya samu mutum 10 daga cikin abokan nasa da ke raye.

“Gaskiya a yadda nake yanzu, lokaci kawai nake jira. Ina fata in bar wannan duniya da imani.

“Ina fata ban saba wa kowa ba a rayuwa, idan kuwa hakan ta faru, ina fata za a yi mini afuwa, ni ma na yafe wa duk wani da ya saba mini.

“A zuri’armu n i kadai na rage, inda nake rayuwa a tsakanin jikoki,” inji Dantata.

Daga nan, ya yaba da ziyarar da aka kai masa, kana ya yi addu’ar samun dauwamammen zaman lafiya ga Nijeriya da al’ummarta.

Tun da farko, Sanata Kashim Shettima ya ce ya je Kano ne ziyarar tuntuba tare da ziyarar dattijon don neman tabarraki a wani bangare na yakin neman zabensu a 2023.

A cikin tawagar dai har da Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, kuma sun ziyarci dattawan jihar kamar su Alhaji Musa Gwadabe da Janar Lawal Jafaru Isah (mai ritaya) da Alhaji Tanko Yakasai a gidajen su.

Monday, 26 December 2022

’Yan Bindiga Sun Sace Manoma 100, Sun Sanya Haraji A Neja

 


’Yan bindiga sun kashe mutum hudu tare da yin garkuwa da mutum fiye da 100 ciki har dakanan yara a Kananan Hukumomin Rafi da Mashegu na Jihar Neja.

Daga cikin wadanda bata-garin suka kashe har da basaraken gargajiya da ’yan banga biyu da wani mutum daya a Karamar Hukumar Mashegu.

Maharan sun kuma sanya harajin Naira miliyan uku-uku domin dakatar da garkuwa da mutane a yankunan kananan hukumomin Rafi da Shiroro inda suka yi awon gaba da mutum 61.

Al’ummar yankunan Rafi da ’yan bindiga suka kai wa hari sun shiga yin kaura zuwa wasu wurare domin samun aminci.

Wani mazaunin yankin ya ce sun daina zuwa gonakinsu saboda tsoron kada a yi garkuwa da su, a yayin da ’yan bindiga ke sace masu amfanin gona.

Hisbah Ta Rufe Wuraren Shan Giya Sama Da 100 A Zariya



Wata kungiyar addinin Musulunci mai zaman kanta mai suna Hisbah, ta jagorance garkame wuraren shan giya sama da 100 a Karamar Hukumar Sabon Gari da ke Jihar Kaduna.

Dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Sabon Gari, Garba Datti Babawo ne ya tabbatar da hakan, yayin gabatar da hsaidar kammala karbar horo ga ’yan kungiyar su 750 da ya gudana a hedkwatar Karamar Hukumar ta Sabon Gari.

Dan majalisar ya ce tun da Karamar Hukumar take ba ta taba samun sa’ida daga ayyukan badala ba sama da lokacin da aka kafa rundunar ta Hisbah.

Daga nan sai Babawo ya ja kunnen dakarun da su tabbatar suna bin dokokin dokoki yayin gudanar da ayyukansu.

Tun da farko sai da Kwamandan rundunar a yankin, Abubakar Auwal ya ce dakarun su 750 sun sami cikakken horo a harkar tsaro kan yadda za su gudanar da ayyukansu.

Kwamnadan ya kuma ce 500 daga cikin dakarun maza ne, yayin da 250 kuma mata ne, kuma za su sadaukar da kawunansu wajen hidimta wa al’umma.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Kosan Waka Passes on as Gov. Yusuf condoles family

The Kano State Government has announced with profound sadness the passing of renowned political singer, Muhammadu Buhari, popula...