Kamfanin MaxAir Zai Ci Dawo Jigilar Aikinsa Na Cikin Gida Najeriya Daga Ranar 30 Ga Watan Yuli
Kamfanin Max Air Limited ya yi farin cikin sanar da dawo da zirga-zirgar jiragen cikin gida daga ranar Lahadi 30 ga Yuli, 2023, biyo bayan dakatarwar da aka yi na wucin gadi saboda rashin tsaro. Kamfanin yayi nuna godiya ga abokan huldarsa masu daraja don fahimtar su da hakuri a wannan lokacin. A sanarwar da shugabannin Kamfanin suka fitar,tace,tsaro yana cikin jigon ƙimar MaxAir Limited, kuma suna ɗaukar alƙawarinsu na amincin fasinja tare da matuƙar mahimmanci. Bayan gudanar da cikakken bincike na cikin gida, an kawo musu rahoton cewa gurbataccen man fetur ya yi tasiri a ayyukansu. Sakamakon haka, ba tare da bata lokaci ba muka fara tantancewa a cikin gida, don kare lafiyar fasinjoji, bisa radin kanmu mun dakatar da ayyukanmu na tsawon kwanaki biyu kafin Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta shiga tsakani. "Muna so mu tabbatar wa dukkan fasinjojinmu cewa muna aiki tuƙuru don magance matsalolin tsaro da aka taso a wannan lokacin dakatarwa. Tawaga...