Dokar Najeriya Ta Haramta Biyan Kuɗin Fansa — Ministan Tsaro
Ministan Tsaro Mohammed Badaru Abubakar ya ce Dokar Najeriya ta haramta biyan masu garkuwa da mutane kuɗin fansa. Ministan wanda ya bayyana haka ne a taron Majalisar Zartarwa da aka gudanar a wannan Larabar, ya ce lokaci ya yi da za a daina biyan kuɗin fansar saboda haka ne kaɗai hanyar kawo ƙarshen masu garkuwa da mutane. Ya ce Shugaban Kasa ya bai wa dukkan hafsoshin tsaro goyon bayan da ya kamata don ganin an kawo karshen garkuwa da mutane da ya yi ƙamari a ƙasar. Tsohon Gwamnan na Jihar Jigawa, ya ce kasancewar dokar Najeriya ta haramta bayar da kuɗin fansa ya sanya bai kamata mutane su riƙa biyan kuɗin ba saboda ba shi da amfani. “Babbar matsalar ita ce yadda mutane ke fitowa a kafafen yaɗa labarai suna neman taimako, har a zo a tara musu kuɗi domin biyan fansa. Hakan bai dace ba. “Idan muka daina biyan kuɗin fansa, sannu a hankali ayyukan masu garkuwa da mutane zai zama tarihi,” in ji Badaru. Dangane da yadda rashin tsaro ke ƙara ta’azzara a Abuja, babban birnin ƙasar da ku...