Posts

Showing posts with the label Sabon Tsari

NAHCON Ta Bullo Da Sabon Tsari Kan Adadin Kwanakin Da Alhazai Zasu Rinka Yi A Madina

Image
Wata sabuwar doka wacce za ta tilasta wa maniyyatan Madina komawa Makkah bayan kwana 5 a birni mafi tsarki za su tashi daga gobe Talata 8 ga watan Yuni 2023. A sanarwar da mataimakin daraktan harkokin yada labarai da dab'i na hukumar, Mousa Ubandawaki ya sanyawa hannu, tace Sabuwar manufar ta zama wajibi ne biyo bayan korafin cunkoson alhazan Najeriya a birnin Madina. Yana da kyau a lura cewa a karon farko cikin dogon lokaci hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta baiwa alhazan Najeriya dari bisa dari damar ziyartar Madina a matakin farko ko kuma kafin Arafat. To sai dai don cimma wannan buri da kuma kawar da takunkumin da aka sanyawa kasar, idan aka samu cunkoson mahajjata a Madina, sai da hukumar ta dauki wannan sabuwar manufa, bayan tuntubar juna da kuma yin nazari mai zurfi. Haka kuma, sanannen abu ne cewa alhazan Nijeriya na zaune ne a unguwar Markaziyya ta musamman a lokacin zamansu, matakin da ya sha yabawa matuka, wanda hukumar ba ta yi niyyar yin sulhu ba. Amma idan