Search This Blog

Showing posts with label Gwamnatin tarayya. Show all posts
Showing posts with label Gwamnatin tarayya. Show all posts

Sunday, 7 April 2024

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Ranakun Hutu

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Talata da Laraba 9 da 10 ga Afrilu, 2024 a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Sallah.

Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da babban sakataren ma’aikatar, Aishetu Ndayako ya fitar ranar Lahadi.

Ministan ya taya daukacin al’ummar musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan mai alfarma.


Tunji-Ojo ya yi kira gare su da su yi koyi da kyawawan dabi’u da suka hada da kyautatawa, soyayya, hakuri, zaman lafiya, makwabtaka, tausayi, kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bayar da misali da shi.
(SOLACEBASE)

Friday, 5 January 2024

Labari Da Dumiduminsa: Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kamfanonin Jiragen Da Zasu Yi Jigilar Maniyyata Hajin 2024

Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da wasu manyan kamfanonin jiragen sama guda uku da za su yi jigilar maniyyata aikin hajjin 2024, wadanda suka hada da Air Peace., FlyNas da Max Air. 

Har ila yau, an amince da wasu kamfanoni uku na jigilar kayayyaki da za su yi jigilar kayan alhazai Waɗannan su ne Cargo Zeal Technologies Ltd, Nahco Aviance da Qualla Investment Limited.
 
A sanarwar da mataimakiyar daraktar harkokin hulda da jama'a da dab'i ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, tace Yarjejeniyar ta karfafa yunƙurin gwamnati na tabbatar da ingantaccen aikin hajji ga maniyyatan Najeriya. 

Don haka, a lokaci guda gwamnatin tarayya ta amince da rabon maniyyata daga jahohi daban-daban ga kowane kamfanonin jiragen sama da aka amince da su kamar haka:
 
i.Air Peace zai yi jigilar maniyyata daga: Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, FCT, Imo, Kwara, Ondo da Ribas.
ii.FlyNas za ta yi jigilar alhazai musulmi daga: Borno, Lagos, Osun, Ogun, Niger, Sokoto, Kebbi, Yobe da Zamfara.

iii. Kamfanin Max Air da ke da kaso mafi tsoka ne zai dauki nauyin jigilar alhazai daga: Bauchi, Benue, Kano, Katsina, Kogi, Nasarawa, Adamawa, Oyo, Taraba, Kaduna, Sojoji, Gombe, Jigawa da Plateau.
 
Rabon maniyyatan ga kamfanonin jirage ya yi daidai da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Najeriya da Saudiyya kan jigilar alhazai a karkashin kason gwamnati. 

A wani labarin kuma, Ministan harkokin wajen Najeriya Ambasada Yusuf Maitama Tuggar na shirin jagorantar wata tawaga daga hukumar alhazai ta kasa NAHCON domin halartar rattaba hannu kan yarjejeniyar aikin hajjin shekarar 2024. a wannan wata na janairu
 
Malam Arabi ya taya murna kamfanonin jiragen sama da aka amince da su a kan zaben da aka yi musu, ya kuma yi kira gare su da su tashi tsaye wajen gudanar da aikin hajji cikin kwanciyar hankali a kakar 2024. Hukumar NAHCON ta ci gaba da sadaukar da kai wajen tabbatar da mafi girman matsayi a harkar aikin hajji, tare da mai da hankali kan aminci da gamsuwar mahajjata.
 

Wednesday, 26 July 2023

Gwamnatin Tarayya ta ce daga watan Satumbar wannan shekara za ta fara ba wa dalibai rance-Mashawarcin Shugaban

Mashawarcin Shugaban Kasa kan Ayyuka na Musamman, Dele Alake, ya kara da cewa gwamnati za ta bullo da sabbin hanyoyin tallafa wa dalibai masu karamin karfi.

“Daga cikin abubuwan da gwamnatin ta tsara na tabbatar da ganin kowane dalibi ya kammala karatunsa a kan lokaci, komai karamin karfin iyayensa, akwai daukar su aikin wucin gadi a makarantunsu, bayar da rance da kuma daukar nauyin wadanda suka cancanta a cikinsu,” a cewarsa.

Alaka ya ce dokar bai wa dalibai rance da Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu za ta fara aiki gabanin shiga sabuwar shekarar karatu mai kamawa a watan Satumba.

Sai dai kuma bai ce uffan ba game da matakai ko shirye-shiryen da gwamnatin ta yi domin tabbatar da hakan.

Ya kuma nesanta Gwamnatin Tarayya da karin kudin rajista da sauransu da jami’o’inta suka yi, inda ya ce, har kwanan gobe ba a biyan kudin makaran a jami’o’in, don haka babu gaskiya a rahoton da wasu kafofin yada labarai suka wallafa cewa gwamnatin ta kara kudin makaranta a jami’o’inta.

Ya bayyana cewa, “Shugaba Tinubu zai ci gaba dayin tsayuwar daka domin cika alkawarinsa na ganin kowane dan Najeriya komai matsayinsa ko karfin iyayensa, ya samu ilimin gaba da sakandare.”

Dele Alaka ya sanar da hakan ne a ranar Laraba, bayan wata kafar yada labarai ta ruwaito cewa Jami’ar Legas, mallakin Gwamnatin Tarayya ta kara kudin karatu da ninki 10 daga N19,000 zuwa N190,250 ga daliban fannin likitanci, dangoginsu kuma zuwa N140,250.

Amma ya ce duk da cewa ba a biyan kudin makanta, makarantun “sukan karbi kudin rajista da na dakunan kwana, na dakunan gwaje-gwaje da sauransu, kuma ya danganta da kowace jami’a; amma wannan ba kudin makaranta ba ne.”

AMINIYA

Thursday, 27 April 2023

Labari Da Dumiduminsa : Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Shirinta Na Janye Tallafin Man Fetur

Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin cire tallafin man fetur a karshen gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Wannan na daga cikin shawarar da majalisar tattalin arzikin kasa ta yanke a zamanta na ranar Alhamis.

Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na Kasa, Misis Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a lokacin da take zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa a karshen taron hukumar zaben da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja.



Zainab ta bayyana cewa akwai yiyuwar cire tallafin zai fara aiki a watan Yuni saboda dokar masana'antar man fetur, PIA da kuma kasafin kudin 2023 sun ba da tallafi har zuwa watan Yuni, don haka duk wani jinkiri na iya buƙatar gyara PIA da tanadin kasafin kuɗi.

Ministan, ya ce babu wani wa'adi da aka bayar na cire tallafin, kuma gwamnati mai zuwa za ta yanke shawara a kan lokacin da za ta iya yin hakan.

Cikakken labarin zai zo muku nan gaba kadan

Wednesday, 4 January 2023

Gwamnatin tarayya za ta dena biyan tallafin man Fetur

 


Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce daga ƙarshen watan Yunin wannan shekara za ta daina biyan tallafin man fetur a ƙasar.

Ministar kuɗi, kasafi da tsare-tsare ta ƙasar Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a lokacin gabatar da kasasfin kuɗin shekarar 2023.

BBC Hausa ta rawaito cewa Misis Zainab ta ce gwamnatin tarayya ta ware kimanin naira tiriliyan 3.36 domin biyan tallafin man fetur ɗin a cikin wata shida na farkon shekarar 2023.

Ministar ta ƙara da cewa hakan na daga cikin tsarin tsawaita cire tallafin zuwa wata 18 da gwamnatin ta bayyana a shekarar da ta gabata.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Head of Service Urges Civil Servants to Uphold Ethical Conduct

The Head of Service, Kano State, has called on civil servants to strictly adhere to the Civil Service ethical code and show grea...