Yau INEC Za Ta Taron Gaggawa Kan Zaben Adamawa
A yau Talata Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) za ta gudanar ta taron gaggawa da ta kira kan dambarwar sakamakon zaben gwamnan Jihar Adamawa da ya tayar da kura. Daga taron ne za a ji shawarar da INEC ta yanke a game da sakamakon zaben gwamnan, wanda a ranar Lahadi hukumar ta dakatar da tattarawa saboda rikicin da ya dabaibaye shi. A ranar Litinin hukumar ta dakatar da Kwamishinan Zabe (REC) na Jihar Adamawa, Barista Hudu Yunus Ari, saboda ya yi gaban kansa wajen ayyana Sanata Aisha Dahiru Binani ta Jam’iyyar APC a matsayin zababbiyar gwamna, alhali ba a kammala tattara sakamakon zaben ba. Lamarin dai ya yamutsa hazo, amma Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, wanda yake neman a zaben a Jam’iyyar PDP, ya bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu, domin INEC za ta dauki matakin da ya dace. Tuni dai Fintiri da PDP da kungiyoyin kare dimokuradiyya suka yi tir da abin da kwamishinan zaben ya yi, inda suka bukaci INEC ta dauki mataki a kan wannan kwamacala. Rikicin zaben ya dauki sabon ...