Dan jarida, Ndace, ya wallafa littatafai uku kan yadda Buratai yai nasarar yaƙi da Boko Haram/ISWAP
Jibrin Baba Ndace, tsohon wakilin jaridar Blueprint a ɓangaren tsaro, ya bayyana cewa ya rubuta littattafai uku ne a kan yaƙi da ta'addanci duba da yadda tsohon Shugaban Hafsoshin Sojojin Ƙasa, COAS, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya), duba da irin jajircewar sa wajen yakin. An ƙaddamar da littattafan, masu taken “Walking the War Front with Lt. Gen. TY Buratai,” “Duty Call Under Buratai’s Command” da kuma “The Lonely Grave and Other Poems" a ranar Asabar da ta gabata a dakin taro na Shehu Musa Yar’adua da ke Abuja. Da ya ke magana game da dalilin da ya sa ya fara aikin wallafa litattafan, wanda ya kwashe shekaru biyar yana rubutawa, Ndace, tsohon babban sakataren yada labarai, CPS, ga Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja, ya lura cewa ya sami kwarin gwiwa da bukatar rubuta littattafan ne na yakin da ake yi da masu tada kayar baya a matsayin sa na ganau ba jiyau ba. “Wadannan littattafan sun samu goyon baya da gudunmawa daga tsoffin sojoji da suka taka ...