Buhari ya yi kira ga 'yan Najeriya su riƙa gode wa Allah

 


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce abubuwan more rayuwa da ake ginawa a faɗin ƙasar 'abin ban sha'awa' ne.

A wata sanarwa mai mai magana da yawun shugaban ƙasar Femi Adesina ya fitar, Shugaba Buhari ya yi kira ga 'yan ƙasar da su riƙa yaba wa da abubuwan more rayuwa da ake gina musu, la'akari da yanayin da ƙasar ke ciki idan an kwatanta da sauran ƙasashe.

Shugaban na jawabi ne a lokacin da yake kammala ziyarar aiki ta yini guda da ya kai jihar Kano da ke arewacin ƙasar domin ƙaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin jihar da ta tarayya da kuma wasu kamfanoni masu zaman kansu suka yi.

Shugaban ya ce ‘‘muna da ƙasaitacciyar ƙasa, amma ba ma yaba mata, har sai mun ziyarci ƙasashe maƙwabta da sauran ƙasashe, inda sai mutane sun yi da gaske sannan su sami abinci sau ɗaya a rana''.

‘‘A lokacin da nake shawagi a cikin jirgi adadin dogayen gine-ginen da na gani da yawan ci gaban da ake da shi a doron ƙasa abin ' ban sha'awa' ne. Mun gode wa Allah, Mun gode wa Allah'', in ji Buhari.

Shugaban ƙasar ya kuma umarci manyan 'yan ƙasar da su ƙarfafa wa matasa gwiwwa wajen rungumar ilimi, yana mai cewa dole ko ana so, ko ba a so makomar ƙasar a hannun matasan take.

Ya ce '‘dole su rungumi ilimi, Fasaha ta saukaka abubuwa da dama, to amma babu abin da zai maye gurbin ilimi, dan Allah ku ƙarfafa wa yara gwiwwa su samu ilimi''.

Shugaban ya kuma jinjina wa gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje bisa ayyukan raya jihar da ya shimfiɗa, yana mai cewa a ziyarar baya-bayan nan da ya kai jihohin Kogi da Yobe da Legas da Katsina ya nuna cewa, gwamnonin waɗannan jihohi sun yi namijin ƙoƙari, wajen yin ayyukan raya ƙasa a jihohin nasu idan aka kwatanta da kuɗaden da suke samu.

(BBC)

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki