Posts

Showing posts with the label Garkuwa da mutane

Karin Dalibai 7 Na Jami'ar Kogi Sun Shaki Iskar 'Yanci

Image
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kogi ta ce an kuɓutar da ƙarin wasu ɗalibai bakwai da aka sace a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Confluence da ke yankin Osara a jihar Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Williams Aya, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis. Aminiya ta ruwaito kamar yadda hukumar ‘yan sandan ta tabbatar cewa an sace ɗalibai 24 a jami’ar kuma zuwa yanzu an ceto 21 daga ciki. Ya ce Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nijeriya, IGP Kayode Egbetokun, ya tura ƙwararru domin ci gaba da aikin ceto ragowar ɗaliban da ke hannun masu garkuwa da su. “An tura sashen tsaro na rundunar ‘yan sanda na sama, wanda ya ƙunshi jami’an rundunar masu amfani da jirgi masu saukar ungulu da aka horar da su kan binciken ta sama da jami’an sa ido da kuma sashen leƙen asiri na fasaha (TIU) don ci gaba da aikin ceton da kuma kai farmaki kan masu aikata laifuka a jihar. “Ƙwararru jami’an tsaro tare da haɗin gwiwa ne suka kai ga ceto ƙarin mutane bakwai (7) da a...

Rashin tsaro: Gwamnatin Kano Tayi Alkawarin Taimakawa Gwamnatin Tarayya Akan Yaki Da Masu Ta'addanci da Satar Mutane

Image
Gwamnatin jihar Kano ta lashi takobin marawa shirin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu baya na dakile illolin rashin tsaro da ke dagula zaman lafiya a kasar nan. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wannan alkawarin ne a ranar Juma’a a lokacin da ya karbi bakuncin ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Alhaji Muhammad Idris a ziyarar ban girma da ya kai gidan gwamnati. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnan ya ce ya dace a hada kai da gwamnatin tsakiya domin dakile wuce gona da iri domin dawo da ci gaban kasa. Alhaji Yusuf ya yabawa shugaba Tinubu bisa yadda ya yi biyayya ga kiran da ya yi na sake bude iyakokin Najeriya da wasu kasashe, matakin da zai taimaka wajen rage wahalhalun tattalin arzikin kasar. Ya kuma bayyana ziyarar a matsayin wacce ta dace da la’akari da yadda ta ke gudanar da harkokinta da masu ruwa da tsaki ciki har da ‘yan kasuwa da suka yi alkawarin yin duk abin da ya kamata na marawa gwamnatin taray...

An Sako Daliban Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ekiti

Image
An sako daliban da malaman nasu ne kimanin mako guda bayan an yi garkuwa da su   Dalibai tara da malamansu da aka yi garkuwa da su a Jihar Ekiti sun kubuta daga hannun ’yan bindiga. Da misalin karfe 2 na dare, kafin wayewar garin yau Lahadi ne masu garkuwa da su suka sako su. Hukumomi a jihar sun tabbatar da sako daliban su tara tare da malamansu. An sako daliban da malaman nasu ne kimanin mako guda bayan an yi garkuwa da su a makarantar Apostolic Faith Group of Schools da ke yankin Emure-Ekiti. Kawo yanzu dai babu bayanin ko an biya kudin fansa. An yi garkuwa da su ne a makarantar Apostolic Faith Group of Schools da ke yankin Emure-Ekiti. (AMINIYA)

An Sako Kannen Nabeehah Da Ke Hannun ’Yan Bindiga

Image
  Da misalin kare 12:30 na daren Asabar ne kannen na Nabeeh suka isa gidansu da ke Abuja, da rakiyar jami'an tsaro. Masu garkuwa da mutane sun sako ’yan uwan marigayiya Nabeeha Al-Kadriyah hudu da suka sace a Abuja bayan sun shafe kwanaki 19 a hannunsu. Da misalin kare 12:30 na daren Asabar ne kannen na Nabeeh suka isa gidansu da ke Abuja, da rakiyar jami’an tsaro. Kawunsu  Sherifdeen, ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho da safiyar Lahadi, “An sako ’yan matan ne da yammacin ranar Asabar kuma tuni sun nufi gida”. Su hudun su ne Najeeba ’ya aji 500 a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da kanwartar da ke aji 300 a jami’ar Nadherah, tare da tagwayen kannensu, Habeeba da Haneesa. Dawowarsu bayan sun shafe kwanaki 19 a hannunsu ’yan bindigar da suka sace su a ranar 2 ga Janairu, 2024 ta sanya murna tskanin al’ummar unguwar. Sanarwar da Sherifdeen ya sanya wa hannu ta ce, “farin cikinmu game da dawowarsu ba zai misaltu ba, muna godi ga Allah da al’umma da suka ba mu gudunmawa. “Muna...

Dokar Najeriya Ta Haramta Biyan Kuɗin Fansa — Ministan Tsaro

Image
  Ministan Tsaro Mohammed Badaru Abubakar ya ce Dokar Najeriya ta haramta biyan masu garkuwa da mutane kuɗin fansa. Ministan wanda ya bayyana haka ne a taron Majalisar Zartarwa da aka gudanar a wannan Larabar, ya ce lokaci ya yi da za a daina biyan kuɗin fansar saboda haka ne kaɗai hanyar kawo ƙarshen masu garkuwa da mutane. Ya ce Shugaban Kasa ya bai wa dukkan hafsoshin tsaro goyon bayan da ya kamata don ganin an kawo karshen garkuwa da mutane da ya yi ƙamari a ƙasar. Tsohon Gwamnan na Jihar Jigawa, ya ce kasancewar dokar Najeriya ta haramta bayar da kuɗin fansa ya sanya bai kamata mutane su riƙa biyan kuɗin ba saboda ba shi da amfani. “Babbar matsalar ita ce yadda mutane ke fitowa a kafafen yaɗa labarai suna neman taimako, har a zo a tara musu kuɗi domin biyan fansa. Hakan bai dace ba. “Idan muka daina biyan kuɗin fansa, sannu a hankali ayyukan masu garkuwa da mutane zai zama tarihi,” in ji Badaru. Dangane da yadda rashin tsaro ke ƙara ta’azzara a Abuja, babban birnin ƙasar da ku...

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sace Jami'in Alhazai A Kano

Image
A daren jiya Asabar ne, wasu mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane ne,suka je har gida suka tafi da Jami'in Alhazai na Karamar Hukumar Bebeji Alhaji Sagiru Umar Kofa, ya kasance babban hadimi ga zababben dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa  Majiyarmu ta tabbatar mana cewa masu garkuwa wadanda suka shiga gidan Sagiru Kofa su biyar, an tabbatar cewa wasu daga cikinsu na dauke da bindiga A halin yanzu dai tuni jami'an 'yan sanda sun dukufa domin gano inda masu garkuwar suka yi da shi don ƙoƙarin kubutar da shi 

'Yan sandan Najeriya sun ceto mutane 58 daga hannun 'yan bindiga

Image
  ‘Yan sanda a Najeriya sun ce sun ceto mutane 58 da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a jihar Kogi, yayin da daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da sun ya rasa ransa yayin artabu tsakanin jami’an tsaro da ‘yan ta’addan A cikin wata sanarwa da kakakin rundinar ‘yan sandan jihar Josephine Adeh ta fitar a wannan Lahadin, ta ce wannan nasara da suka samu wani bangare ne na aikin hadin gwiwa tsakanin rundunar da sauran jami’an tsaro, tare da hadin gwiwar ‘yan banga da mafarautan jihar.  Adeh ta ce lamarin ya faru ne a dajin Udulu da ke Karamar Hukumar Gegu mai nisan kilomita 145 daga bababban birnin tarayya kasar.  A cewarta, an yi musayar wuta tsakanin ‘yan ta’addan da kuma jami’an tsaro kuma daga bisani suka tsere suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su.   Sai dai bata bayyana inda aka sace mutanen ba da kuma tsawon lokacin da suka dauka a hannun ‘yan ta’addan.   RFI

'Yan bindigar da suka yi garkuwa da ni suna so su isarwa da gwamnati wani sake ne - Kanal 'Yandoto

Image
 

Labari da dumiduminsa : 'Yan bindiga sun sake yin garkuwa da fasinjojin Jirgin kasa

Image
Watanni bayan da ‘yan ta’addan suka kai hari tare da yin garkuwa da fasinjoji da dama a cikin jirgin kasa zuwa Kaduna, wasu ‘yan bindiga sun kuma kai farmaki tashar jirgin kasa tare da kwashe mutane da yawa a Jihar Edo dake kudu maso kudancin Najeriya. Fasinjojin da suka samu raunuka, an ce suna jiran su hau jirgin kasa a wurin da lamarin ya faru, kafin su nufi garin Warri mai arzikin man fetur. Tuni dai hukumar 'yan sanda ta Rahotanni sun tabbatar da faruwar lamarin a cewar tashar talabijin ta TVC. Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta ce ‘yan bindigar da ke dauke da bindigogi kirar AK-47 sun kai farmaki tashar jirgin da misalin karfe 4 na yammacin ranar Asabar 7 ga watan Janairu, inda suka yi ta harbe-harbe kafin su fito da shirinsu.  A ranar 28 ga Maris, 2022 ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan jirgin kasa da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, inda suka kashe wasu tare da yin awon gaba da wasu fasinjoji. 2022 . Har yanzu dai Hukumar Jiragen kasa ta Najeriya ba...