Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Yi Ga NAHCON Da Ta Samar Canjin Dala Kan Farashin Gwamnati Ga Maniyyata
Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa, ya bukaci Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta kara zage damtse wajen ganin an samu dala a farashin gwamnati ga wadanda zasu halarci aikin hajjin bana. A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya bayyana hakan ne a wata ganawa da kungiyar Arewa New Agenda a wata ziyarar wayar da kai da hukumar alhazai ta kasa suka kai Kano, wanda aka gudanar a ofishinsa. Ya kara da cewa karin kudin aikin Hajjin bana da kuma karancin lokacin biyan kudi na daga cikin matsalolin dake kawo tsaiko wajen biyan kudaden ajiya. Da yake mayar da jawabi kan wadannan matsalolin, shugaban tawagar kungiyar Arewa New Agenda daga Hukumar Alhazai ta kasa, Dakta Muhd Lawan Salisu, ya tabbatar wa darakta Janar din cewa, sun dukufa wajen hada kai da hukumomin da abin ya shafa, ciki har da Sarkin Musulmi, domin mika kokon bara ga