Posts

Showing posts with the label Hukumar Tace Finafinai

Hukumar Tace Finafinai Ta Rufe Sutudiyon Mawaki Ɗanzaki

Image
Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa ita ce ta garƙame sutudiyon mawakin siyasar nan Idris Ɗanzaki tare da yin awon gaba da kayan aikinsa. Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Abdullahi Lawan Sulaiman ya shaida wa ’yan jarida a Kano cewa hukumar ta ɗauki matakin ne bayan mawaƙin ya yi biris da gayyatar da ta yi mana na bayyana a ofisoshint Ya ce tun ranar Asabar Hukumar ta nemi mawakin ya bayyana a ofisoshinta, amma har zuwa lokacin da muke kawo muku wannan labari bai amsa gayyatar ba. “Kasancewar a yanzu zamani ya sawwake abubuwa mun yi amfani da waya inda muka kira wannan mawaki Idris Ɗanzaki inda kuma muka nemi ya zo wannan hukuma. “Bayan sun kira ni a waya sun ce suna gayyata ta, na tura lauyana hukumar don ya wakilce ni. “Amma me zai faru sai aka kira ni cewa wai hukumar ta rufe sutudiyona haka kuma ta kwashe wasu kayayyakin aikina.” Abdullahi Lawan ya kara da cewa hakan ya sa Hukumar ta sa aka kulle sutudiyon tare da kwashe kayayyakin aikin...

Dawo Da Makarantar Koyar Da Sana'ar Fim Dake Tiga, Babbar Nasara Ce Ga Masana'antar Kannywood- Abba El-Mustapha

Image
Shugaban Hukumar tace Fina-finai da Dab'i ta Jahar Kano, Abba El-mustapha ya bayyana farin cikinsa tare da karfin gwiwa dangane da kara bude makarantar koya Sana'ar Fina-finai dake garin Tiga a Jahar Kano. A sanarwar da jami'in hulda da jama'a na Hukumar,  Abdullahi Sani Sulaiman  ya sanyawa hannu, tace nada sabon Daraktan Makarantar Alh. Dr. Maigari Indabawa yace, hakika abu ne da ya dace duba da yadda Sana'ar fina-finan ke bukatar sauyi ta fannin ilimi Wanda hakan zai bunkasa tattalin arzikin Kano tare da kawo kudin shiga. Ya Kara da cewa, da yawa daga cikin yan masana'antar na bukatar Samin karin horo domin a nuna musu sabbin da baru ta yadda  Sana'ar zata tafi da zamani haka kuma su kansu yan masana'antar zasuyi gogayya da takwarorin su na kasashen waje . Abba El-mustapha ya godewa Gwamna tare da yiwa sabon shugaban makarantar fatan alheri tare da addu'ar Allah yasa yafara a sa'a ya Kuma gama lafiya. El-mustapha ya kuma yi wa saur...