Alhajin Kano Dake Jinya A Makkah Ya Rasu
Daraktan Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano Alh Laminu Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan ne a karamar hukumar Gaya yayin da ya jagoranci tawagar shugabannin hukumar domin sanarwa iyalansa tare da yi musu ta'aziyya A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, Laminu Rabi'u Danbappa, ya kara da cewa, cike da bakin ciki muke sanar da rasuwar Alh Umar Hamza daya daga cikin alhazan mu da ya rage a Asibitin Saudiyya. Umar Hamza, mai shekaru 75 ya rasu ne a Asibitin Saudiyya a jiya bayan gajeruwar jinya, kamar yadda Hukumar Kula da Asibitin Saudiyya ta tabbatar. Laminu Danbappa, wanda ya bayyana alhinin rasuwar Alh Umar Hamza, ya bayyana marigayin a matsayin malamin islamiyya, yana jajantawa 'yan uwa akan wannan rashi. Daraktan Janar din a madadin gudanarwar hukumar, ya mika ta’aziyyarsa ga Jafar Umar Hamza, dan marigayin, da sauran ‘yan uwa da suka rasu, da kuma daukacin al’ummar Musulmi. Laminu...