Gwamnatin Najeriya Na Zargin Peter Obi Da Cin Amanar Kasa
Gwamnatin Tarayya ta shawarci dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar LP a zaben da ya gabata, Peter Obi, da ya guji tunzura jama’a su tayar da zaune tsaye kan sakamakon zaben da ya gabata. Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayar da shawarar yayin wata tattaunawarsa da kafafen yada labarai a birnin Washington DC na Amurka. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Ministan ya je Amurka ne don tattaunawa da kafofin kan abubuwan da suka wakana yayin zaben da ya gabata a Najeriya. NAN ya ce ya zuwa yanzu, Ministan ya tattauna da jaridar Washington Post da Muryar Amurka da mujallar Foreign Policy da kuma kamfanin dillancin labarai na AP. Lai Mohammed ya kuma gargadi Peter Obi da cewa ba daidai ba ne ya rika neman hakkinsa a kotu, sannan kuma ya rika kokarin tayar da zaune tsaye a daya bangaren. “Obi da Mataimakinsa Datti, bai kamata su rika yi wa zababben Shugaban Najeriya, Bola Tinubu na APC barazana cewa muddin aka rantsar da shi ranar 29 ga w