Hajin 2024: Hukumar Alhazai Ta Bauchi Ta Bayyana Farin Cikinta Bisa Yadda Maniyyata Suka Je Asibitoci Domin Yi Musu Rigakafi
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Bauchi ta bayyana jin dadinta kan yadda maniyya suka fita domin karbar allurar rigakafi A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Muhammad Sani Yunusa ya sanyawa hannu, yace Sakataren zartarwa na hukumar limamin Abdurrahman Ibrahim Idris ya bayyana haka a lokacin da yake karbar rahoton aikin rigakafin da ake yi daga kananan hukumomin jihar 20. Ya ce an fara gudanar da aikin ne a jiya Lahadi 11 ga watan Mayu, 2024 tare da maniyyatan karamar hukumar Bauchi da sauran kananan hukumomin da ke kusa da babban birnin jihar kamar Dass, Tafawa Balewa, Bogoro, Alkaleri, Kirfi da Ganjuwa Imam Abdurrahman ya kara da cewa maniyyatan wadanda ke nesa na kananan hukumomin Katagum, Gamawa da. Zaki, sun fita da yawa zuwa manyan asibitocinsu daban-daban domin ayi musu rigakafin, yana mai bayyana yadda lamarin ya kasance abin karfafa gwiwa. Don haka yay Kira ga maniyyatan da har yanzu ba a yi musu allurar ba da su yi hak...