Posts

Showing posts with the label Jaririya

Bakuwa Ta Sace Jariri Awa 3 Da Haihuwarsa A Asibiti

Image
  Ana zargin bakuwa ta sace jaririn ne da hadin bakin ’yar uwar mai jegon Wata mata ta sace jariri awa uku bayan haihuwarsa a Asibitin Kwararru na Dalhatu Arafat (DASH) da ke garin Lafia, Jihar Nasarawa. Ana zargin bakuwar ta sace jaririn ne da hadin bakin ’yar uwar mai jegon sa’o’i kadan da haihuwarsa ta hanyar yi wa mahifiyarsa tiyata. Aminiya ta gano bayan haihuwarsa da misalin karfe 3 na asubahin ranar Talata ne jami’an asibiti suka mika jaririn da mai jegon ga wata ’yar uwarta domin ta ci gaba da kula da su. Wani ganau da ya nemi a boye sunasa ya ce, bayan sun dawo dakin masu jego ne ’yar uwar mai jegon ta kawo mata da wata bakuwa, wadda ake zargin sun hada baki wajen sace jaririn. ‘Kamar Layar Zana’ A cewarsa, “’yar uwar mai jegon ce ta ce mata za ta koma gida ta dauko cajar wayarta da ta manta; shi ne ta hada ta da wata mata da za ta zauna da su kafin ta dawo ,” wadda ake zargin ita ce ta sace jaririn. Sace jaririn daga dakin masu jegon da misalin karfe 6 na safe,  awa ...