Posts

Showing posts with the label Kwamitoci

Shugaban Kungiyar Kano Pillars Ya Rusa Dukkanin Kwamitocin Da Shugabancin Baya Ya Kafa

Image
Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta bayyana wani gagarumin sauyi a bangaren gudanarwa sakamakon sauyin shugabanci da aka samu a baya-bayan nan.  A sanarwar da Sashen yada labarai na kungiyar ya fitar, tace Sabon shugaban kungiyar da aka nada Alhaji Ali Muhammad Umar ya bayar da umarnin rusa dukkanin kwamitocin da tsohuwar hukumar ta kafa. A cewar shugaban ta hannun sashen yada labarai da sadarwa na kungiyar, daga nan take, an rusa dukkanin kwamitocin da suka gabata.  A cikin rikon kwarya, dukkan ayyukan kwamitin za su kasance karkashin kulawar sakataren kungiyar Malam Abbati Sabo.  Wannan tsari na wucin gadi zai ci gaba da aiki har sai sabuwar hukumar ta kafa sabbin kwamitoci a kan lokaci. Wannan shawarar ta nuna aniyar kulob din na daidaita ayyuka da kuma tabbatar da samun sauyi a sabuwar gwamnati.  Shugaban kungiyar ya nuna kwarin guiwa kan yadda Malam Abbati Sabo ke da ikon kula da wadannan ayyuka tare da jaddada cewa sake fasalin kungiyar na da n...