Posts

Showing posts with the label Cefanarwa

Gwamnati Za Ta Cefanar Da Asibitin Fadar Shugaban Kasa

Image
Gwamnatin Tarayya ta fara shirin cefanar da Asibitin Fadar Shugaban Kasa da wasu sassa da ke karkashin fadar gwamnatin ga ’yan kasuwa. Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa, Tijjani Umar, ya ce Ma’aikatar Kudi da Kasa tare da Fadar Shugaban Kasar sun ware wasu ayyuka da tsare-tsare uku a Fadar Shugaban Kasa da gwamnati za ta fara yin hadaka da ’yan kasuwa wajen gudanar da su. Wutar Lantarki: Minista ya ba da umarnin dawo da wutar Kano ’Yan bindiga sun kashe mutum 40 a Kebbi da Zamfara Ya bayyana cewa Asibitin Fadar Shguaban Kasa da ke Abuja da Legas daya ne daga bangarorin da ake shirin shigo da ’yan kasuwa su zuba jari. Sauran su ne Sashen Kula da Gandun Daji da kuma Dandalin Wasan Yara na Fadar Shugaban kasa. ’Yan Najeriya na yawan yin ce-ce-ku-ce game da yadda Shugaba Buhari ke zuwa duba lafiyarsa a kasashen waje. A watannin baya dai Gwamnatin Tarayya ta yi kokarin yin dokar hana jami’an gwamnati zuwa duba lafiyarsu a kasashen waje, da nufin inganta yanayin bangaren lafiy...