Posts

Showing posts with the label Tallafin man Fetur

Za Mu Yi Fito-Na-Fito Da Gwamnati Kan Cire Tallafin Man Fetur - Kungiyar Kwadago

Image
Kungiyar kwadagon Najeriya ta sha alwashin yin fito na fito da gwamnatin kasar a kan yunkurin da sabon shugaban Najeriyar ke yi na janye tallafin mai. Kungiyar ta ce ba za ta amince ba, saboda janye tallafin zai jefa al'umma a cikin wahala. Tun bayan sanarwar da shugaba Tinubu ya yi a ranar da aka rantsar da shi aka fara dogayen layukan mai a sassan kasar. Kwamarade Nasir Kabir shi ne sakataren tsare-tsare na Kungiyar NLC ya shaida wa BBC cewa shugaban Najeriyar ya yi hanzarin sanar shirin cire tallafin man fetur ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ba. "Kafin ka janye tallafi sai ka kawo wutar lantarki, tituna duk sun wadata talakawa sun rabu da talauci a kasa, ake maganar gwamnati ba ta hannu a cikin wannan abu", in ji shi. Kungiyar ta yi ikirarin a cikin sa'o'i bayan sanarwar shugaban kasa alummar kasar sun tsinci kansu cikin wani hali na tsaka mai wuya saboda an fuskanci karancin man fetur a wasu sassan kasar da karin farashin mai inda a wasu wur

An fara cinkoson sayen fetur a Lagos sakamakon kalaman Tinubu

Image
An fara dogayen layuka a gidajen sayar da man fetur da ke birnin Lagos na Najeriya jim kadan da sanarwar da shugaban kasar, Bola Ahmed Tinubu ya yi ta janye kudin tallafin man fetur. An fara cinkoson sayen fetur a Lagos sakamakon kalaman Tinubu An fara dogayen layuka a gidajen sayar da man fetur da ke birnin Lagos na Najeriya jim kadan da sanarwar da shugaban kasar, Bola Ahmed Tinubu ya yi ta janye kudin tallafin man fetur. Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, direbobin motoci sun yi cincirindo a gidajen mai na NNPC da ke Ikeja, inda suke rige-rigen sayen man. Jaridar ta rawaito cewa, da dama daga cikin gidajen man fetur masu zaman kansu ba sa sayar da man ya zuwa lokacin da Daily Trust ta fitar da rahoton. A yayin gabatar da jawabinsa na shan rantsuwar kama aiki a yau Litinin, shugaba Tinubu ya bayyana cewa, mawadata ne kadai ke amfana da kudin tallafin man fetur din a maimakon talakawa. Tinubu ya ce, gwamnatinsa za ta karkatar da kudin tallafin zuwa ga bangarorin ilimi da

Labari Da Dumiduminsa : Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Shirinta Na Janye Tallafin Man Fetur

Image
Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin cire tallafin man fetur a karshen gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari. Wannan na daga cikin shawarar da majalisar tattalin arzikin kasa ta yanke a zamanta na ranar Alhamis. Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na Kasa, Misis Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a lokacin da take zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa a karshen taron hukumar zaben da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Zainab ta bayyana cewa akwai yiyuwar cire tallafin zai fara aiki a watan Yuni saboda dokar masana'antar man fetur, PIA da kuma kasafin kudin 2023 sun ba da tallafi har zuwa watan Yuni, don haka duk wani jinkiri na iya buƙatar gyara PIA da tanadin kasafin kuɗi. Ministan, ya ce babu wani wa'adi da aka bayar na cire tallafin, kuma gwamnati mai zuwa za ta yanke shawara a kan lokacin da za ta iya yin hakan. Cikakken labarin zai zo muku nan gaba kadan

Gwamnatin tarayya za ta dena biyan tallafin man Fetur

Image
  Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce daga Æ™arshen watan Yunin wannan shekara za ta daina biyan tallafin man fetur a Æ™asar. Ministar kuÉ—i, kasafi da tsare-tsare ta Æ™asar Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a lokacin gabatar da kasasfin kuÉ—in shekarar 2023. BBC Hausa ta rawaito cewa Misis Zainab ta ce gwamnatin tarayya ta ware kimanin naira tiriliyan 3.36 domin biyan tallafin man fetur É—in a cikin wata shida na farkon shekarar 2023. Ministar ta Æ™ara da cewa hakan na daga cikin tsarin tsawaita cire tallafin zuwa wata 18 da gwamnatin ta bayyana a shekarar da ta gabata.