Posts

Showing posts with the label Dr Ahmad BUK

Dokta Ahmad BUK: Ba rabo da gwani ba

Image
Sahabi Aliyu (RA) ya fadi ga Jabir dan Abdullahi (RA) cewa “Duniya ta dogara ne a kan abu hudu; addini da malami mai yin aiki da iliminsa, sai jahili wanda ba ya girman kai wajen neman sani da kuma mawadaci wanda ba ya rowa da dukiyarsa.” Marigayi Sheikh Dokta Ahmad Muhammad Ibrahim wanda aka fi sani da Dokta Bamba ya ce ilimi ba komai ba ne sai sanin abu a zuciya da kuma gaskata shi a zahiri, yayin da jahilci ke nuni da kiyaye abu a zuciya wanda a zahirance ba gaskiya ba ne. Saboda haka, a cewarsa ba kawai rashin sanin abu ake kira jahilci ba, a’a har ma da sani gami da riko da abin da bai gaskata ba. Rayuwa irin ta Dokta Ahmad madubi ce ga daukacin al’ummar Musulmi. M utum ne mai kyakkyawar fahimta ga lamurran addini, amma mai zafafawa wajen kare martabar Annabi Muhammad (SAW). Mai kimanin shekara 82 a duniya, wanda ya rasu a ranar Juma’a, 7/1/2022, marigayi Dokta Ahmad Bamba ya shafe daukacin rayuwarsa wajen nema da kuma yada ilimi. Ya shafe sama da shekara 20 yana dauka...