Posts

Showing posts with the label Kasida

Kasidar European Champions League - Professor Salisu Shehu

Image
Da sunan Allah Shi Daya Zan fara bayani bai daya.  Rabbu Kai Tilo ne Kai Daya Ba kama a gareKa gaba daya. Duk halittun kas da samaniya Kai ne Ka yiwosu gaba daya. Rabbana saita mini zuciya Nai bayani ba wata zamiya Nai salati na yo tahiya GA Abin kaunarmu gaba daya.  Al--Bashiru Aminin duniya  Ka ji Mai cetonmu gaba daya.  Ni nufina zan yi matashiya Ga shababu su bar sharholiya.  Watakila a yo mini tambaya,  Kan batun me zaka matashiya?  Kan batun kwallon Birtaniya,  Wofin banza na Pirimiya.  KO batun kwallo na Spaniya,  La Liga abin hauragiya.  Ga Juventus can ta Italiya, Wadansu kanta suke ta hayaniya.  Masu sonta su ce mata gimbiya  Ba karatu sai dai tankiya Wasu har Azumi fa suke niyya,  Don sadaukarwa ga Spaniya,  KO su yo yankar qurbaniyya,  Zallar kaunar Barceloniya.  David Beckham tuni ya riya,  Baya son Ummah Islamiyya,  Haka ma Chelsean Birtaniya,  Basu son jinsin If...