Kofa ya shirya taron addu'a na musammam ga Tinubu, Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf
...Ya ce har yanzu ƙofar NNPP a buɗe take don yin ƙawance da APC da sauran jam’iyyu Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Kiru da Bebeji, Kano, a yau ya tara malamai 1,000 a garinsa na Kofa a Bebeji, Kano, domin addu’a ta musamman ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da kasar baki daya, Jagoran jam’iyyar NNPP da Ɗarikar Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, PhD, FNSE da kuma neman nasara ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a Kotun Ƙoli, da kuma addu’ar neman taimakon Allah ga ɗan majalisar. A sanarwar da hadimin dan majalisar kan harkokin yada yada labarai, Sani Ibrahim Paki ya sanyawa hannu, yace yayin taron, malaman sun sauke Alƙur’ani sau 1,101, sannan suka yi addu’o’i na musamman. A taƙaitaccen jawabin da ya gabatar a wajen taron, Hon. Jibrin ya ce alaƙarsa da Shugaba Tinubu ba ɓoyayya ba ce. Ya kuma ce Kwankwaso ne maigidanshi, sannan zai ci gaba da iya ƙoƙarinsa wajen ganin an samu kyakkyawar alaƙa a tsakanin Tinubun da Kwankwaso.