Posts

Showing posts with the label Alkalan Babbar Kotu

Gwamna Yusuf Ya Nada Alkalan Babban Kotu 9, Khadis 4 Na Kotun Daukaka Kara.

Image
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da manyan alkalan kotuna tara, da Khadis na kotun daukaka kara ta Shari’a 3 bisa Shawarar majalisar shari’a ta kasa (NJC), da kuma amincewar majalisar dokokin jihar Kano. A wata sanarwa da mai magana da yawunsa Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya bayyana wadanda aka nada a matsayin alkalan babbar kotuna sune; Justice Fatima Adamu, Justice Musa Ahmad, Justice Hauwa Lawan, Justice Farida Rabi'u Dan Baffa, Justice Musa Dahiru Muhammad da Justice Halima Aliyu Nasir. Sauran su ne; Justice Aisha Mahmud, Justice Adam Abdullahi, da Justice Hanif Sunusi Yusuf. Yayin da wadanda aka nada a matsayin Khadi kotun daukaka kara ta Shari’a sune; Khadi Muhammad Adam Kademi, Khadi Salisu Muhammad Isah, Khadi Isah Idris Said, da Khadi Aliyu Muhammad Kani. Da yake jawabi ga Alkalan kotun daukaka kara da Khadis na kotun daukaka kara ta Shari’a a wajen bikin rantsuwar da aka gudanar a dakin taro na Africa House dake gidan gwamnati, Gw...