Zan tattauna da masu tayar da kayar baya idan na zama shugaban kasa - Peter Obi
Ɗan takarar gwamna a Jam'iyyar Labour a Najeriya Peter Obi ya ce zai buƙaci ya tattauna da duk wani ɗan gwagwarmaya ko kuma masu tayar da ƙayar baya da gwamnatin Najeriya ta ɗaure idan ya samu mulkin ƙasar. Mista Obi ya bayyana haka ne a wani zauren tattaunawa da tambayoyi da gidan talabijin na Channels a Najeriya ya shirya ga ɗan takarar da mataimakinsa. Ko da wani ya tambayi Mista Obi ko cikin waɗanda zai tattauna da su har da ƴan Boko Haram da ke jawo matsaloli a arewacin Najeriya da kuma ƴan ƙungiyar IPOB da ke kudu maso gabashin ƙasar, sai ya ce " Zan tattauna da dukansu, ko ma wace irin bindiga ce suke ɗauke da ita". Mista Obi ya ce ko da mutum yana ɗaure a gidan yari ne zai je ya fito da shi domin su zauna su tattauna. Mista Obi ya ce ya yanke hukuncin yin haka ne domin ganin cewa an samu zaman lafiya a ƙasar. "Zan tattauna da waɗanda suke so a tattauna da su. Sai an kalli me ke jawo suke gwagwarmaya; batu ne na rashin adalci ko lamari ne na talauc...