Posts

Showing posts with the label Jahohi

Yanzu-yanzu: NAHCON ta raba kujerun aikin Hajjin 2024 ga Jihohi, Abuja da bangaren rundunar soja

Image
Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta raba kujeru ga jihohi talatin da shida da babban birnin tarayya Abuja da kuma rundunonin soji domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2024. Takardar da Hajj Reporters suka gani a ranar Talata ta nuna cewa jihar Kaduna ce ta samu kaso mafi tsoka na kujeru 6004 sai jihar Kano da ta samu 5934. Sokoto ta samu 4996 a matsayi na uku yayin da jihohin Kebbi da Katsina suka samu 4752 da 4513. Duba cikakken jadawalin yadda rabon kujerun ya kasance (IHR)

DA DUMI-DUMI: Sake fasalin Naira: Kotun Koli ta Dage Sauraron karar da Kaduna, Kogi da Zamfara suka shigar

Image
Kotun kolin Najeriya ta dage ci gaba da shari’ar kan manufar musanya naira na babban bankin Najeriya CBN zuwa ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu domin sauraron kararrakin da jihohi 10 suka hada.   Kotun kolin da ta saurari karar a ranar Larabar da ta gabata ta cika makil da wasu manyan lauyoyi da sauran gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi, Nasir El-Rufai da Yahaya Bello, bi da bi.   A zaman da ya gabata, Kotun ta dakatar da aiwatar da wa'adin ranar 10 ga watan Fabrairu na CBN daga yin kwangilar tsohuwar takardar kudi ta N200, N500 da N1,000.   Jihohin Zamfara da Kogi da kuma Kaduna ne suka shigar da karar gwamnatin tarayya da kuma babban bankin kasa CBN.   Sauran jihohin da suka hada da Neja, Kano, Ondo, Ekiti, su ma sun nemi a shigar da su gaban CBN da gwamnatin tarayya.     An fara zaman kotun inda mai shari’a John Okoro ya jagoranci kwamitin mutum bakwai.   Ya ce bai kamata kotu ta yi watsi da shari’ar da kuma manufarta ba domin ya shafi ’yan Najeriya d...

Hajj2023: Hukumar NAHCON Ta Bawa Kano Kujerun Hajji 2,902

Image
Rabon ya kasance kamar haka: Abia 53 Adamawa. 2669 Anambara. 39 Bauchi. 3, 132 Bayelsa. 35 Binuwai. 236 Borno. 2,735 Cross Rivers. 66 Delta 74 Nassarawa. 1,567 Nijar. 5,165 Ogun. 1,139 Ondo 436 Osun. 1,054 Oyo. 1 441 Yobe. 1,968 Ebony 117 Edo 274 Ekiti. 197 Enugu. 40 FCT 3,520     Gombe. 2,301 Imo. 30 Jigawa. 1,525 Kaduna. 5982 Kano. 5,902 Katsina. 4,913   Kebbi. 4871 Kwara. 3,219 Legas. 3,576 Plateau. 1,984 Rivers. 50 Sokoto. 5,504 Taraba. 1,590 Za a saki jihar Kogi ne bayan kammala nazarin ayyukanta yayin da aka dakatar da rabon jihar Akwa Ibom saboda rashin sabunta lasisin aiki. A halin da ake ciki, ana sa ran dukkan jihohin za su mika wa Hukumar biyan kashi 50% na kudin kujerun 2022 kafin ranar 10 ga watan Fabrairu.  Rashin yin hakan ka iya sanyawa a rage yawan adadin kujerun da aka bawa jahar      HANNU Mousa Ubandawaki Mataimakin Daraktan Labarai da wallafe-wallafe NAHCON, Abuja