Posts

Showing posts with the label Paris

Tinubu Ya Gana Da Ganduje A Abuja

Image
  Shugaban kasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, ya gana da Gwamnan Jihar Kano mai barin gado, Abdullahi Umar Ganduje a gidansa na Defense House da ke Abuja. Da yammacin Asabar ɗin nan dai Ganduje ya shiga sahun waɗanda suka taro Asiwaju Tinubu lokacin da ya sauka Abuja daga ƙasar Faransa. Bayan an isa gida kuma sun yi ganawar sirri tsakaninsu. Ganawar dai ba ta rasa nasaba da ƙorafin da Ganduje yake da shi game da ganawar Asiwaju Tinubu da tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso a birnin Paris. A baya-bayan nan dai aka ji wani sautin hirar wayar tarho na yawo inda Ganduje ke kukan zaɓaɓɓen shugaban ƙasar bai kyauta masa ba da ya yi wannan tattaunawar. Kawo yanzu dai Ganduje bai bayyana wa manema labarai matsayar da suka cimma da Asiwaju Tinubu ba . AMINIYA

Da dumi-dumi: Kwankwaso yayi ganawar sa’o’i hudu da Tinubu a birnin Paris

Image
Zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya yiwa jam’iyyar NNPP a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, sun yi ganawar akalla sa’o’i hudu a birnin Paris na kasar Faransa a ranar Litinin, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito. A tsakiyar tattaunawar, TheCable ta fahimci cewa, akwai yuwuwar shigar Kwankwaso cikin gwamnati mai zuwa yayin da Tinubu ke shirin kafa “gwamnatin hadin kan kasa” – wanda ke nufin bai wa jam’iyyun adawa wasu mukamai a cikin gwamnatin. Taron ya kuma tattauna batutuwan da suka shafi zaben shugabannin majalisar kasa, gabanin kaddamar da majalisar ta 10 a ranar 13 ga watan Yuni. Zaben gwamnan kano: Inda aka Kwana game da karar APC da NNPP a Kotu An fara taron Paris tsakanin Tinubu da Kwankwaso ne da karfe 12:30 na rana kuma aka kammala da karfe 4:45 na yamma, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida wa jaridar TheCable. Ko Kun zabi aiki ko ba ku zaba ba, mun yi titin Kurna babban layi ne saboda All...