Posts

Showing posts with the label Taron Karawa Juna Sani

Kwamishinan Lafiya na Kano Ya Bukaci Hukumomin Su Yi Koyi Hukumar KSCHMA

Image
Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya yi kira ga Hukumomin da ke karkashin ma’aikatar su yi koyi da kokarin Hukumar Kula da yajejeniyar Lafiya ta Jihar Kano (KSCHMA) na bunkasa ko sake duba kundin aikinsu domin samar da ingantaccen kiwon lafiya a jihar. Kwamishinan ya yi kiran ne a yayin taron bita na kwanaki 3 da KSCHMA tare da hadin guiwar shirin Lafiya suka shirya domin samar da tsarin yi wa Hukumar hidima domin inganta aiwatar da shirin bayar da gudunmawar kiwon lafiya. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mohammad Nura Yusuf, jami’in yada labarai na KSCHMA a ranar Juma’a. A nata jawabin babbar sakatariyar hukumar ta KSCHMA, Dakta Rahila Aliyu Mukhtar, ta bayyana cewa, hukumar ta gudanar da ayyukanta na samar da ayyukan kiwon lafiya mai sauki da kuma tallafa wa mazauna jihar Kano domin shawo kan matsalar kudi wajen kafa takardar lissafin magani, da samar da kundin tsarin hidima. yana da mahimmanci. Dokta Rahila ta kar...

Hukumar NAHCON Za Ta Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Akan Kula Da Aikin Hajji

Image
A ci gaba da shirye-shiryen gudanar da aikin hajjin shekarar 2023, hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta shirya taron bita na yini daya kan kula da aikin hajji a dakin taro na gidan alhazai a ranar Asabar. Shirin mai Taken Bayar da Horo da Ƙarfafa nagartar aiki ga Shugabannin Æ™ungiyoyin a aikin Hajji" ana sa ran babban darakta kuma mai ba da shawara kan harkokin Hajji da Umrah a Saudiyya, Dr. Badr Muhammad Al solamin zai gabatar da jawabi a yayin taron.  A sanarwar da mataimakin daraktan harkokin yada labarai da hulda jamaa na hukumar, Mousa Ubandawaki, y ace Sauran wadanda zasu gabatar da jawabi sun hada da: Dr. Mohammed Shokri Zamzami, Babban Darakta na Kwamitin Tawwaf na Alhazai da Jamrat Grouping a Muassassah, Abdullah Hammadu Adam, Jami'in Gudanarwa, Muassassah. Sama da Mahalarta 90 ne ake sa ran za su halarci taron, wanda ya kunshi mambobi da shuwagabannin Kungiyar shugabannin hukumomin kula da Dadin Alhazai ta Jihohi, Manyan Jami’an Gudanarwa na kamfafonin jigi...