Posts

Showing posts with the label Kannywood

Kungiyar Kannywood Ta Bawa Kwamishinan Kudi Na NAHCON Lambar Yabo

Image
Da yake jawabi, jagoran tawagar Alhaji Ahmed Kaka ya taya hukumar murnar kammala aikin Hajjin 2023 cikin nasara duk da kalubalen da ake fuskanta. A sanarwar da Shafi'i Sani Muhammad na sashen yada labarai da Dab'i na Hukumar NAHCON ya sanyawa hannu, Shugaban kungiyar ya yi kira da a hada kai a tsakanin bangarorin guda biyu musamman ta fannin wayar da kan alhazai da tsawaita amfani da kafafen sada zumunta na zamani. Kungiyar ta baiwa Alhaji Nura Hassan Yakasai, Kwamishinan kudi lambar yabo ta taimakon jin kai bisa gudunmawar da ya bayar wajen bayar da muhimmin taimako ga marasa galihu a cikin al’umma. Alhaji Yakasai wanda ya bayyana jin dadinsa ga dandalin ya tabbatar musu da shirye-shiryen Hukumar na yin bincike da hada kai da kungiyar nan gaba. Tunda farko da yake nasa jawabin, Shugaban Hukumar NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya yi kira ga ‘yan wasan kwaikwayon Najeriya da su ci gaba da amfani da kafar sadarwar su wajen wayar da kan ‘yan Nijeriya musamman Alh

Dawo Da Makarantar Koyar Da Sana'ar Fim Dake Tiga, Babbar Nasara Ce Ga Masana'antar Kannywood- Abba El-Mustapha

Image
Shugaban Hukumar tace Fina-finai da Dab'i ta Jahar Kano, Abba El-mustapha ya bayyana farin cikinsa tare da karfin gwiwa dangane da kara bude makarantar koya Sana'ar Fina-finai dake garin Tiga a Jahar Kano. A sanarwar da jami'in hulda da jama'a na Hukumar,  Abdullahi Sani Sulaiman  ya sanyawa hannu, tace nada sabon Daraktan Makarantar Alh. Dr. Maigari Indabawa yace, hakika abu ne da ya dace duba da yadda Sana'ar fina-finan ke bukatar sauyi ta fannin ilimi Wanda hakan zai bunkasa tattalin arzikin Kano tare da kawo kudin shiga. Ya Kara da cewa, da yawa daga cikin yan masana'antar na bukatar Samin karin horo domin a nuna musu sabbin da baru ta yadda  Sana'ar zata tafi da zamani haka kuma su kansu yan masana'antar zasuyi gogayya da takwarorin su na kasashen waje . Abba El-mustapha ya godewa Gwamna tare da yiwa sabon shugaban makarantar fatan alheri tare da addu'ar Allah yasa yafara a sa'a ya Kuma gama lafiya. El-mustapha ya kuma yi wa saur