Posts

Showing posts with the label Murabus

Labari da dumiduminsa : Shugaban APC Na Kasa Sanata Abdullahi Adamu Ya Ajiye Mukaminsa

Image
A ranar Lahadin da ta gabata ne shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu ya sanar da yin murabus daga mukaminsa na shugaban jam’iyyar. New Telegraph ta tattaro daga majiya mai tushe cewa Sanata Adamu ya yi murabus ne bisa umarnin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Hakazalika, Sakataren jam’iyyar na kasa, Iyiola Omisore shi ma ya mika takardar murabus din sa bayan mintuna kadan. Idan dai za a iya tunawa, Adamu, tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa ya fuskanci fafutuka da dama tun bayan da jam’iyyar ta lashe zaben shugaban kasa a ranar 25 ga Fabrairu, 2023. Da take magana game da ci gaban, Prime Business Africa (PBA) a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli ta ce ta samu tabbacin da ba a bayyana ba daga majiya mai tushe a cikin jam’iyya mai mulki da fadar shugaban kasa cewa Adamu “ya yi murabus ‘yan mintoci kadan da suka gabata bisa umarnin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.” To sai dai kuma tsohon shugaban da ke fama da rikici ya sanya ranar 19 ga watan Yuli za a gudanar da taron kwamiti...