Posts

Showing posts with the label Harry

Yarima Harry na Burtaniya ya zargi yayansa Yarima Williams da dukansa

Image
Yarima Harry ya yi da'awar cewar yayansa Yarima William ya taɓa dukan sa, in ji jaridar Guardian, wadda ta ce ta ga wani ɓangare na littafin da yarima Harry ɗin ke rubutawa, mai taken 'Spare'. Jaridar ta ruwaito cewa littafin ya ambato wani lokaci da aka samu sa-in-sa tsakanin ƴan'uwan biyu a kan matar Harry, Meghan. Jaridar ta ce a cikin littafin Harry ya rubuta cewa "ya ci kwalata, ya tsinka sarƙar da ke wuyana, sannan ya bugani da ƙasa." Sai dai Majiyarmu ba ta kai ga ganin littafin na 'Spare' ba. Ba za a buga littafin ba sai ranar Talata ta sama, amma jaridar Guardian ta ce ta ga littafin a wani abu da ta kira " bugun kafin a wallafa". Kawo yanzu fadar Buckingham ba ta ce komai ba, duk da cewa an tuntuɓe ta kan batun.bayar da rahoto kan lamarin, ba mu kira shi da faɗa ba, saboda Harry bai mayar da martani ba. A cewar jaridar Guardian "Yarima Harry ya rubuta cewar ɗan uwansa ya nemi da ya rama bugun da ya yi masa, amma ya ...