Posts

Showing posts with the label Tattaki

Dan Jarida Ya Mutu Yana Tattakin Zuwa Wurin Aiki Saboda Karancin Takardun Kudi

Image
  Wani fitaccen dan jarida da ke aiki a gidan rediyon Ibadan, ya riga mu gidan gaskiya a kan hanyarsa ta zuwa wurin aiki a safiyar wannan Asabar din. Ma’aikacin jaridar wanda aka fi sani da Baba Bintin, ya yanke jiki ne ya fadi matacce kamar yadda wakilinmu ya ruwaito. Bayanai sun ce lamarin ya faru ne yayin da Baba Bintin ke hanyarsa ta zuwa gidan rediyon Fresh FM, inda zai gabatar da wani shiri tare da wasu takwarorinsa, Komolafe Olaiya da Olalomi Amole a yankin Challenge da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo. Baba Bintin dai ya shahara wajen gabatar da shirin bayyana farashin kayayyaki da ranakun cin kasuwannin yau da kullum a fadin jihar da kewaye. Rahotanni sun tabbatar da cewa karar kwana ta cimma Baba Bintin yayin da yake tattaki tun daga unguwarsu ta Amuloko zuwa Challenge sanadiyyar rashin tsabar kudi a hannu da zai biya masu ababen hawa na haya. Jama’a a Najeriya na ci gaba da babatu kan halin kunci da suka shiga tun bayan sauya fasalin takardun kudi da Babban Bankin Kasar CB