Hajj2023 : Hukumar NAHCON Ta Kaddamar Da Tawagar 'Yan Jaridu
Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ya kaddamar da tawagar kafafen yada labarai na kasa domin gudanar da aikin Hajji na shekarar 2023 a kasar Saudiyya. Taron ya gudana ne a ofishin da ke Abuja ranar Alhamis. Hassan ya jaddada mahimmancin bin ka'idojin Æ™wararru, gami da daidaito a aikin jarida. Ya taya ‘yan tawagar murna da aka zabo su, ya kuma bukace su da su dauki kansu a matsayin abokan hadin gwiwa da NAHCON wajen gudanar da aikin Hajji ba tare da wata matsala ba. Shugaban hukumar ya bayar da tabbacin cewa za a kwashe dukkan maniyyatan da suka yi rajista a jirgi a kan lokaci, inda ya ce jami’an NAHCON za su tafi kasar Saudiyya ranar 21 ga watan Mayu domin yin shirye-shiryen da suka dace. Ya nanata kudurin hukumar na tabbatar da cewa alhazai sun samu kimar kudinsu kuma an dauke su cikin gaggawa. Da yake magana kan da rawar da kafafen yada labarai ke takawa, shugaban NAHCON ya yi kira ga kungiyar kafafen yada labarai