Saudiyya Ta Kwashe ’Yan Najeriya Da Suka Makale A Sudan Zuwa Kasarta
Gwamnatin kasar Saudiyya ta kwashe wasu daga cikin ’yan Najeriya da suka makale a yakin da ya barke a Sudan zuwa kasarta. Minista a Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya, Zubairu Dada, ya ce Saudiyya ta tura jiragen ruwa da suka kwashe ’yan Najeriya zuwa birnin Jeddah na kasarta, bayan barkewar yaki a Sudan. Ma’aikatar ta ce daga bisani za a maido da ’yan Najeriyan da aka kai Saudiyya gida, kuma gwamnatin Tarayya na kokarin ganin cewa babu dan Najeriya ko daya da ya rage a Sudan kafin cikar wa’adin awa 72 da bangarorin da ke yaki da juna suka bayar na tsagaita wuta. Ta bayyana cewa a kokarinta na kwashe ’yan Najeriya da suka makale bayan barkewar yakin, Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira miliya 552 kan daukar hayar motocin da za su fitar da su zuwa iyakar Sudan da kasar Masar. Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Geoffrey Onyema, ya ce an dauki hayar bas-bas 40 da za su kwashi ’yan Najeriya daga Khartoum, babban birnin Sudan zuwa iyakar kasar Masar da ke Aswan, inda za su hau jirgi zuwa gi