HAJJIN 2023: Rikicin Sudan Ka Iya Kawo Matsala Ga Jigilar Ahazan Najeriya - Kungiyar Fararen Hula
Rikicin da ake fama da shi a kasar Sudan na iya kawo cikas ga jigilar maniyyatan Najeriya zuwa kasar Saudiyya cikin sauki, domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2023, in ji kungiyar daukar rahotannin aikin hajji mai zaman kanta. Kungiyar farar hula a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma'a mai dauke da sa hannun shugabanta na kasa Ibrahim Muhammad, ta ce tuni yakin ya kai ga rufe sararin samaniyar Sudan ba zato ba tsammani. Kungiyar ta ce Najeriya "dole ne ta hanyar NAHCON ta yi gaggawar sake duba kalubalen da ke gabanta sannan ta fito da wasu zabin da za a yi a matsayin ma'auni." Kamar yadda jadawalin NAHCON ya nuna, za a fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa kasa mai tsarki a ranar 21 ga Mayu, 2023. Jiragen saman jigilar alhazan Najeriya na tafiya ta sararin samaniyar Sudan a lokacin da suke tafiya Saudiyya, kuma ana daukar matsakaicin sa'o'i hudu zuwa biyar kafin su isa kasar. Sai dai kuma rufe sararin samaniyar kasar Sudan ba z...