Search This Blog

Showing posts with label TCN. Show all posts
Showing posts with label TCN. Show all posts

Tuesday, 8 August 2023

Gwamnatin Kano Za Ta Tallafawa Kamfanin TC Don Bunkasa Samar Da Wutar Lantarki A Kano-Dantiye

Gwamnatin jihar Kano ta himmatu wajen yin amfani da dukkan hanyoyin da za su bunkasa samar da wutar lantarki don ci gaban masana'antu.

A sanarwar da daraktan harkokin cikin gida na Ma'aikatar, Usman Bello ya sanyawa hannu, Ta tace Kwamishinan yada labarai Baba Halilu Dantiye ne ya bayyana hakan, a yayin da yake gabatar da jawabi a lokacin da ya karbi bakunci tawagar mataimakin Janaral Manaja na ofishin Kamfanin Dakon wutar lantarki dake Jahar Kano 

Kwamishinan ya ce Gwamna Abba Kabir a shirye yake ya ba hukumar TCN dauki domin kammala ayyukanta daban-daban a jihar.

Ya kuma yi nuni da cewa, babu wata gwamnati da za ta yi watsi da damar da za ta samar da wutar lantarki ga al’ummarta, duba da irin dabarun da take da shi wajen bunkasa harkokin tattalin arziki a jihar.

Daga nan sai Dantiye ya bada tabbacin GGM na goyon bayan ma’aikatar wajen fadakar da al’umma kan ayyukanta.

Tun da farko a nasa jawabin, Mataimakin Janaral Manaja na shiyyar Kano Muhammad Kamal Bello ya ce sun je ma’aikatar ne domin neman goyon bayan gwamnatin jihar Kano wajen gudanar da ayyukanta.

Ya bayyana cewa jihar Kano duk da yawan al’umma da tattalin arzikinta a kasar nan na da layukan sadarwa guda biyu kacal yayin da sauran jihohin ke da takwas.

Mal muhammad Kamal Bello ya ce akwai ayyukan watsa labarai da tashoshin sadarwa daban-daban da aka shafe sama da shekaru takwas ana aiwatarwa.

Ya daga cikin abubuwan da ke kawo cikas a ayyukan sun hada da rufe hanyoyin sadarwa da dama wadanda ke yaki da fadada layukan.

Sauran batutuwan sun hada da samar da filayen ayyukan kananan tashoshin Danbatta da Walalanbe da hukumar TCN ta bayar, in ji Mal Bello.

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnati da ta sa baki wajen aiwatar da ayyukan.

Sunday, 30 April 2023

Wutar Lantarki: Katse Layin KEDCO A Kano Somin-Tabi Ne —TCN

Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Kasa (TCN) ya ce katse wutar da ya yi wa Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na KEDCO a Jihar Kano somin-tabi ne.

Wasu sassan Jihar Kano sun yi kwanaki a cikin duhu bayan TCN ya katse layin wutar da suke kai saboda taurin bashin da yake bin KEDCO.

TCN ya katse wasu layikan wutar KEDCO mai kula da jihohin Kano da Jigawa da Katsina bayan kokarinsa na ganin kamfanin ya biya bashin ya faskara.

Mataimakin Janar-Manajan TCN na Shiyyar Kano, Bello Muhammad da kuma kakakin KEDCO, Sani Bala Sani, sun tabbatar cewa TCN ya katse wutar a ranar 26 ga watan Afrilu da muke ciki.


Layukan wutar da TCN ya kashe a Kano su ne Club Road da CBN da kuma Flour Mills (Dan Agundi), wanda hakan ya jefa yankunan da ke samun wuta daga nan a cikin duhu na tsawon kwanaki.

Tun ranar 24 ga watan ranar 24 ga wata Babban Jami’in Kasuwanci na TCN, E. A. Eje ya sanar cewa, “TCN ya ba da umarnin katse wutar KEDCO saboda saba ka’idar biyan bashi.”

Ya bayyana cewa katse layikan somin-tabi ne kafin TCN ya katse wutar gaba daya idan kamfanin bai biya bashin ba.

Ya bayyana cewa katse layikan somin-tabi ne kafin TCN ya katse wutar gaba daya idan kamfanin bai biya bashin ba.


Ya ce, “Mun riga an sanar da KEDCO da duk wadanda ake bi bashi game da saba alkawarin nasu; Mun kuma wallafa a jarida inda muka bayyana ranar da za mu yanke musu wuta bisa tsarin kasuwancin, kuma har wa’adin ya wuce.”


Amma mai magana da yawun KEDCO, Sani Bala Sani, ya ce, “Duk da haka, kamfanin na aiki tare da TCN da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin an daidaita nan ba da jimawa ba.”

Sani ya ba wa jama’a hakuri, da alkawarin tabbatar da sama musu wutar lantarki mai inganci.
AMINIYA 

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

FG Urges KOICA, FAO to Align Agricultural Intervention with Nigeria’s Development Priorities, Ward-Based Strategy

The Federal Government has called for stronger alignment between development partners’ interventions and Nigeria’s national deve...