Za a shafe wata shida nan gaba cikin karancin Fetur a Najeriya - Inji IPMAN
Kungiyar dillalan man fetur a Najeriya ta ce za a ci gaba da fuskantar karancin fetur a faɗin kasar har zuwa watan Yunin wannan shekarar. Kungiyar ta ce wahalhalun ko karancin na da alaƙa da shirin gwamnati na janye tallafin mai baki daya a cikin watan Yuni. Tun a shekarar da ta gabata al'ummar kasar ke fama da karanci mai a sassa daban-daban na Najeriya, musamman arewaci. A ranar Litinin ministan albarkatun fetur, Timipre Sylva, ya ce kamfanin mai na NNPC na tafka asara kan farashin da ake sayar da man a yanzu. A makon da ya gabata, ministan kudi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, ya ce gwamnatin Tarayya ta ware naira tiriliyan 3.6 domin biyan tallafi zuwa Yunin 2023.