Posts

Showing posts with the label FAAN

Hajj2024: NAHCON Ta Ja Hankalin Hukumar Kula Da Filayen Jiragen Kan Samar Da Kayayyakin Da Suka Wajaba

Image
Hukumar Alhazai ta kasa ta hori hukumar dake lura da filayen jiragen sama ta kasa, da ta gaggauta samar da dukkanin kayayyakin da suka waja a bangare tashin alhazai da nufin gudanar da jigilar alhazan na wannan shekarar cikin nasara A sanarwar da mataimakin Daraktan yada labarai da dab’I na hukumar , Mousa UIbandawaki ya sanyawa hannu, yace Mai rikon mukamin shugabancin hukumar, Malam Jalal Ahmed Arabi, shi ne yayi wannan kiran lokacin da wakilin hukumar na bangaren aikin Haji suka kai masa ziyarar ban girma a Abuja Ya bayyana cewa samar da kayayyakin da suka wajaba a bangaren tashin alhazan dake fadin kasar nan zai taimaka matuka gaya wajen samun nasarar aikin jigilar alhazan ‘’Ku manyan abokan hula ne wajen gudanar da aikin Haji. Koda yake akwai wasu abubuwa da ake la’akari dasu yayin tashin alhazai kuma muna sa ran zaku sanar mana yanayin da filiyen jiragen saman da ake amfani dasu waje n tashin alhazai suke ciki’’ Ya bayyana cewa kwamitin ya kamata yay duba da lokaci d