Posts

Showing posts with the label Albashi

Kungiyar Kwadayo Ta Yi Watsi Da Naira 48, 000 A Matsayin Mafi Karancin Albashi

Image
Ƙungiyar Ƙwadago NLC ta yi fatali da tayin naira 48,000 da Gwamnatin Tarayya ta gabatar a matsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikata a ƙasar. Mambobin ƙungiyar ta NLC a wannan Larabar su bayyana mamakin dalilin da gwamnati da mambobin kamfanoni masu zaman kansu ke tozarta su da abin da ta bayyana a matsayin tayi mai ban dariya. Aminiya ta ruwaito cewa a yayin da Gwamnatin Tarayya ta miƙa tayin Naira 48,000, ‘yan ƙungiyoyi masu zaman kansu sun miƙa tayin N54,000. Sai dai ƙungiyar NLCn ta bayyana adawartwa kan duk tayin da ɓangarorin biyu suka gabatar a wani taron tattaunawa da aka gudanar a babban Ofishin NLC na Labour House da ke Abuja. Shugabannin ƙwadagon sun ce gwamnati ba ta gabatar da wasu bayanai da za su goyi bayan tayin da ta gabatar ba.

Gwamnatin Kano Ta Yi Alkawarin Mayar Da Karin Albashin Shekara-Shekara Ga Ma'aikata

Image
Gwamnatin jihar Kano karkashin Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta yi alkawarin dawo da biyan  karin kudaden da ake biyan ma’aikata a duk shekara, nan take bayan an gudanar da aikin tantance ma’aikata da tantance bayanan da aka yi. A sanarwar da daraktan wayar da kan al'uma na hukumar, Bashir Habib Yahaya ya sanyawa hannu, yace Babban Akanta Janar na Jihar Kano, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam ne ya bayyana hakan a lokacin wani taro da masu ruwa da tsaki kan yadda ake gudanar da aikin tantancewa da daukar bayanan ma'aikatan  Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa tun bayan amincewar majalisar zartarwa ta jiha na gudanar da aikin da kuma abin da gwamnan jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar, nan da nan aka fara shirye-shirye tare da kara zage damtse don ganin an gudanar da aikin. Ya ci gaba da cewa, gwamnatin jihar ta amince da kwamitoci biyu na dindindin kan aikin biyan albashin ma’aikata a matakin jiha da kananan hukumomi baya ga ‘yan fansho. A nasa jawabin kwamishinan kudi d...

Sanatoci Sun Sallama Albashinsu Na Disamba Ga Mutanen Tudun Biri

Image
Sanatocin Najeriya gaba dayansu sun sadaukar da albashinsu na watan Disamba ga mutanen da harin bom da jirgin soji ya samu a wurin taron Mauludi a Jihar Kaduna. Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya sanar cewa sanatocin su 109 sun amince a ba da albashin nasu a matsayin gudunmuwar ga mutanen Tudun Biri. Sanata Barau wanda ya yi bayani a yayin ziyararsu fadar gwamnatin Kaduna domin jajanta wa Gwamna Uba Sani kan tsautsayi, ya bayyana cewa albasjin ya kama Naira miliyan 109. Ya ce hakika sun yi bakin ciki bisa tsautsayin da ya auka wa al’ummar garin na Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi, kuma majalisar ta sha alwashin yin bincike domin gano musabbabin abin da ya faru. Gwamna Uba Sani a jawabinsa ya mika godidyarsa ga dukkan ’yan majalisar da suka jajanta masa, inda ya bukaci su tabbatar da Hakimin Yan Tudun Biri ya fito kunya ta hanyar yi musu adalci. Ya kumu nuna rashin jin dadinsa bisa yadda wasu ke neman sanya rigar addini ko kabilanci a kan ab...

Saudiyya Ta Yi Wa Messi Tayin Ninkin Albashin Ronaldo

Image
  Kungiyoyin kwallon kafa a kasar Saudiyya na zawarcin gwarzon dan wasan duniya, Lionel Messi, na kungiyar PSG, da tayin albashin da ya zarce na kowane dan wasa a duniya. Rahotanni sun nuna cewa wata kungiya da ke zawarcin Messi a Saudiyya ta yi masa tayin albashin Naira biliyan 183.5 (Dala miliyan 400) a shekara, idan kwantaraginsa ya kare da PSG a wata mai zuwa. Kafar labarai ta Telegraph ta kasar Birtaniya ta ce dan wasan ya fara tunanin duba tayin kuma tuni kungiyar ta fara tattaunawa da Kyaftin din na kasar Argentina kan kwangilar da take masa tayi, bayan dakatarwar da PSG ta yi masa. Idan hakan ta tabbata, Messi zai rika karbar kusan ninki biyun albashin babban abokin hamayarsa Cristiano Ronaldo, wanda a halin yanzu Al Nassr ta kasar Saudiyya ke biyan sa Naira biliyan 96.3 Dala miliyan 210 a shekara, zuwa 2025. A halin yanzu dai, Cristiano Ronaldo ne dan wasa mafi albashi a duniya, inda Messi ke biye da shi, kafin Kylian Mbappe na Farasan da PSG. Wannan sabuwar ta taso ne bay...

Kotu ta umarci Bankin Guarantee Ya Biya N5.7m Da Muhuyi Rimingado Daga Asusun Gwamnatin Kano

Image
Kotun ma'aikata ta kasa da ke Abuja ta umarci Bankin (GT) da ya biya korarren shugaban hukumar KORAFE-KORAFE jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Rimingado, kudi N5,713,891.22 daga asusun albashi na gwamnatin jihar. Adadin kudaden da  Rimingado ke bin gwamnatin ne na albashin ma’aikata, bayan dakatar da shi a watan Yulin 2021. DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa gwamnatin jihar ta dakatar da Mista Rimingado ne bayan bude bincike kan wasu kwangiloli da ake zargin an baiwa wasu kamfanoni masu alaka da iyalan gwamnan. A zaman da aka ci gaba da yi a ranar Talatar da ta gabata, Bankin ta bakin lauyansa Joshua Shekwolo ya shaida wa kotun a cikin wata takardar neman sahalewa cewa gwamnatin jihar Kano ta na da asusun ajiyar banki da jimillar kudaden da suka kai N5,713,891.22 kasancewar an toshe hukuncin da aka yanke kan lamarin. a cikin asusun. Da yake bayar da cikakkiyar umarnin, mai shari’a O.O Oyewumi ya umarci GTBank ya biya kudin a asusun Mista Rimingado...