CBN Ya Zargi Bankuna Da Boye Sabbin Takardun Kudade
B abban Bankin Najeriya (CBN) ya zargi wasu bankuna da yi masa zangon kasa ta hanyar boye sabbin takardun kudade tare da ci gaba da bayar da tsofaffi. Hakan na zuwa ne yayin da ya rage kwana 10 a daina amfani da tsofaffin kudaden kwata-kwata a kasar nan. Babban Jami’in bankin a Jihar Ribas, Maxwell Okafor, ne ya yi zargin a Fatakwal, babban birnin Jihar lokacin da ya jagoranci ayarin CBN yayin ziyarar duba yadda bankuna da kasuwannin Jihar ke ta’ammali da sabbin kudaden ranar Juma’a. Ya ce tsakanin ranakun Alhamis da Juma’a kawai, CBN ya ba bankunan kasuwancin da ke jihar tsabar kudin da suka kai Naira biliyan hudu da rabi, inda ya nuna damuwa kan yadda har yanzu jama’a ba sa samun su. Ya ce, “Mun jima muna sanya idanu a kan yadda ake ba da sababbin kudade, kuma abin da muka gano ba ya karfafa mana gwiwa. “Mun ziyarci wasu bankuna, kuma daya daga cikinsu har yanzu yana bayar da tsofaffin kudi. Wasu injinan ATM dinsu kuma ba sa aiki, kuma mun ji cewar ko kafin mu karaso nan, CBN ya ba s...