Gobara Ta Barke A Gidan PDP
Ga dukkan alamu gobara ta sake barkewa a gidan babbar jam’iyyar adawa ta kasar nan wato PDP, wadda ta sake shiga rudu, makonni kadan da faduwarta a zaben Shugaban Kasa. A ranar Talata da ta gabata ce, Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar na Kasa (NWC), ya ayyana Ambasada Iliya Umar Damagum a matsayin Shugaban Riko na jam’iyar ta kasa. Kafin nadinsa, Alhaji Iliya Damagum shi ne Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Shiyyar Arewa. Kakakin Jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba ne ya bayyana nada Damagun a ranar Talata a wani taron manema labarai a Abuja. A sanarwar da PDP ta fitar, ta ce ya zame mata dole ta yi biyayya ga umarnin wata kotu da ta bukaci Shugaban Jam’iyyar na Kasa Dokta Ayu Iyorchia ya daina bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan kararsa da aka kai gabanta. Wata Babbar Kotu a Jihar Benuwai ce ta dakatar da Dokta Iyorchia Ayu daga shugabancin Jam’iyyar PDP ta Kasa. Alkalin Kotun, Mai Shari’a W.I Kpochi ne ya bayar da umarnin a rana...