Search This Blog

Showing posts with label Ma'aikatar Walwala Da jin kai. Show all posts
Showing posts with label Ma'aikatar Walwala Da jin kai. Show all posts

Monday, 8 January 2024

Labari Da Dumiduminsa: Shugaba Bola Ahmed Tinubu Ya Dakatar Da Ministar Harkokin Walwala Betta Edu

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya dakatar da ministar jin ฦ™ai, Betta Edu nan take.

Kakakin shugaban Najeriyar, Ajuri Ngelale ne ya sanar da matakin dakatar da ministar cikin wata sanarwa da aka fitar a yau.

Shugaba Tinubu ya ษ—auki matakin ne domin ba da dama ga hukumar EFCC mai yaฦ™i da cin hanci da rashawa ta gudanar da bincike a kanta.

Tun farko al'ummar Najeriya sun yi ta matsa lamba inda suke kiraye-kiraye gwamnati ta dakatar da ita daga mukaminta domin a gudanar da cikakken bincike a kanta game da zarge-zargen da ake mata.

Ana zargin ta da bayar da umarnin tura kuษ—i kimanin naira miliyan 585 zuwa asusun bankin wata mata.

(BBC HAUSA)

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Kano Business Community Endorses Gov. Yusuf for Second Term

The leadership of the Kano business community, comprising representatives of 25 major markets across the state, has endorsed Gov...