Posts

Showing posts with the label Biyayya

Gwamna Ganduje ya bayyana Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin Mutum mai Biyayya da Amana

Image
Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan a yayin taron yakin neman zaben jam'iyyar APC a kananan hukumomin Sumaila da Takai. Ya kuma bukaci al’ummar kananan hukumomin biyu da su zabi dan takarar gwamna na jam’iyyar APC da abokin takararsa domin dukkansu an gwada su kuma an amince da su. Gwamnan ya bayyana cewa su biyun sun cancanci a zabe su saboda irin nasarorin da suka samu a ma’aikatun gwamnati daban-daban da suka yi aiki a tsawon shekaru. Dakta Ganduje ya yi nuni da cewa Dr. Nasiru Yusuf Gawauna da Alhaji Murtala Garo sun cancanta haka kuma su sukafi da cewa su gajeshi domin ci gaba da ayyuka da shirye-shiryen gwamnati a bangarori daban-daban da Gina dan Adam. Ya kuma bayyana fatansa na cewa ‘yan takarar na da kwarewa wajen fito da manufofi da shirye shirye da kuma aiwatar da karin manufofi da tsare-tsare da suka shafi ci gaban jihar, idan har aka ba su wa’adi a babban zabe mai zuwa. Gwamnan ya yi amfani da damar wajen yin kira ga masu zabe da su kada kuri...