Posts

Showing posts with the label Kasashen waje

Shugaba Buhari ya gargaɗi ƙasashen ƙetare kan zaɓen Najeriya

Image
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya gargaɗi gwamnatocin ƙasashen ketare kan tsoma baki ko katsalanda a harkokin cikin gidan ƙasar musamman a lokutan zaɓe da ke tafe kasa da kwanaki 42. Majiyarmu ta rawaito cewa Shugaban ya sanar da hakan ne lokacin da yake maraba da sabbin jakadun Switzerland da Sweden da Jamhuriyar Ireland da Thailand da Senegal da Sudan ta Kudu a fadar gwamnati. Shugaban ya ce Najeriya tana aiki kafada-kafada da kungiyar ƙasashen yammacin Afirka Ecowas domin shawo kan matsalolin tsaro da bijiro da matakan tabbatar da zaɓe mai sahihanci ba tare da katsalanda ga kudin tsarin mulkin kasa ba. Ko a shekarar da ta gabata sai dai shugaba Buhari ya yi irin wannan gargadi inda yake cewa burinsa shi ne ganin anyi sahihin zaɓe cikin kwanciyar hankali. Abin da ya faɗawa jakadun Wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar ta rawaito shugaba Buharin ya gargadin jakadun ketare kan su mayar da hankali kan abin da ya shafesu da dalilan turo su Najeriya, da kuma ka