Posts

Showing posts with the label Rantsar da Tinibu

Zan Turo Wakilai Da Za Su Halarci Bikin Rantsar Da Tinubu — Joe Biden

Image
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce zai turo wakilan gwamnatinsa da za su halarci bikin rantsar da sabon Shugaban Najeriya Bola Tinubu. Biden, ta wata sanarwa a shafin gwamnatin Amurka ranar Litinin, ya ce tuni sun kafa tawagar mutane tara karkashin jagorancin Sakatariyar Raya Gidaje da Birane ta Amurka, Marcia L. Fudge da za su halarci bikin rantsuwar a Abuja, babban birnin Najeriya. Sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta za ta fara aiki a Sudan —MDD An samu kamfanin Facebook da laifin sayar wa Amurka bayanan jama’a Wannan sanarwar na zuwa ne kwanaki kadan bayan sukar da tsohon dan takarar Shugaban Kasa na PDP Atiku Abubakar ya yi wa kasar, bayan da Sakataren Gwamnatin Amurka, Antony Blinken, ya taya Tinubu murnar cin zabe. Atiku ya ce sabanin matsayin da gwamnatin Amurka ta bayyana wa duniya kan zaben da ta ce tana sane da irin magudin da aka tafka, bai kamata a ce ta amince wa zaben ba wanda akasarin al’umma suka yarda yana cike da magudi. Baya ga wakilan Shugaban Amurkan, tsoff