Posts

Showing posts with the label Majalisar Wakilai

APC za ta yi zaman gaggawa kan shugabanci a majalisar dokokin Najeriya

Image
  A ranar Laraba 10 ga watan Mayu ne kwamitin gudanarwa na jam`iyyar APC zai yi wani zaman gaggawa kan rikicin neman shugabanci a majalisar dokoki ta goma da za a kafa. A farkon makon nan ne jam'iyyar ta fitar da wata sanarwa da ke nuna ta kebe shugabancin Majalisar Dattawa da ta Wakilai ga wasu shiyyoyin kasar. A sanarwar, APC ta ware wa shiyyar Kudu Maso Kuduncin Najeriya kujerar Shugaban Majalisar Dattawa tare da ayyana sunan Sanata Godswill Akpabio a matsayin wanda zai rike wannan mukamin. Sai kuma kujerar Kakakin Majalisar Wakilai wacce jam'iyyar ta bayyana sunan Tajudeen Abbas daga shiyyar Arewa maso Yammacin kasar. Bisa ga dukkan alamu wannan matakin na jam'iyyar bai yi wa wasu 'ya'yanta dadi ba lamarin da ya sa wasu daga cikinsu yunkurin bijire mata. Wannan hali da ake ciki ne zai sa kwamitin gudanarwa na jam`iyyar ta APC ya gudanar da zaman gaggawar domin nemo bakin zaren warware matsalar. Wani bincike da BBC ta gudanar ya gano tuni wasu masu takarar kujera

Majalisar Najeriya ta gayyaci ministoci kan bacewar gangunan danyen mai

Image
  Kwamitin Majalisar Wakilan Najeriya da ke bincike kan zargin batar gangar danyen mai miliyan 48 a kasar ya gayyaci Ministocin Kudi da na Shari'a da wasu manyan shugabannin hukumomin kasar domin bayar da bahasi a game da wannan badakalar.  Da yake magana kan rashin girmama gayyatar da kwamitin ta ya yi wa Ministocin Kudi da na Shari'a da wasu jami'an hukumomin gwamnatin kasar, Shugaban Kwamitin Binciken Hon. Mark Gbillah, ya ce ana zargin Ministar Kudi Zainab Ahmed da karya dokar gwamnati ta tsarin fallasa masu yi wa gwamnati zagon kasa ta hanyar kin biyan masu fallasawar adadin kudin da ya dace a ba su.   Tun a watan Disamban shekarar da ta gabata ne Majalisar ta yanke shawarar fara bincike kan bantan miliyoyin gangar man, wadanda ake zargin wasu manyan jami'an gwamnatin kasar da karkatarwa zuwa China.     Ya ce a daya bangaren kuma, ana zargin Ministan Shari'a na kasar da karbar kudade daga ketare ba tare da sanyawa cikin asusun gwamnati ba.    Ya kuma bayyana ce

A Karhse Dai Emefiele Ya Bayyana A Gaban Kwamitin Majalisar Wakilai Kan Batun Sababbin Kudi

Image
A ranar Talata ne gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ya gurfana gaban kwamitin majalisar wakilai, inda suke binciken yadda aka yi musanya da Naira. A halin yanzu dai kwamitin da tawagar CBN na gudanar da taro a majalisar dokokin kasar. An fara taron ne da misalin karfe 12:05 na rana bayan shafe sama da awa daya a sirrance. Idan dai za a iya tunawa majalisar da kwamitin sun yi barazanar kama wasu da dama a ranar Alhamis bayan Mista Emefiele ya kauracewa majalisar. Shugaban bankin na CBN ya sanar da tsawaita wa’adin canza canjin kudin zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu. Sai dai kwamitin ya dage cewa dole ne Emefiele ya bayyana a gabansu. A lokacin da aka fara taron, Shugaban Kwamitin, Ado Doguwa ya ce shugaban CBN ya bayar da dalilan rashin amsa gayyata a baya. Cikakken labarin zai zo muku nan gaba kadan  SOLACEBASE