Za a haramta amfani da cokali da farantin soso a Ingila

...

Gwamnmati a Ingila ta tabbatar da cewa za ta haramta kayan cin abinci waɗanda ake amfani da su sau ɗaya ana jefarwa, kamar cokali da farantan soso.

Ba a san yaushe ne harmacin zai fara aiki ba, amma hakan na zuwa ne bayan irin wannan yunƙuri a yankunan Wales da Scotland.

Sakatariya mai kula da harkar muhalli, Therese Coffey ta ce za a yi hakan ne saboda a kare muhalli domin amfanin al'ummar da za ta zo nan gaba.

Masu hanƙoro sun yi maraba da shirin, sai dai sun buƙaci a ɓullo da ƙarin hanyoyin rage amfani da robobi

Alƙaluma sun nuna cewa a ƙasar ta Ingila kowane mutum na amfani da aƙalla farantin cin abinci na roba guda 18 da kuma cokula da wuƙaƙen cin abinci 37 a kowace shekara, inda kashi 10% na irin waɗannan robobi ne kawai ake sake sarrafa su.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki