Messi da Mbappe da Neymar sun yi wasa tare karon farko bayan kofin duniya

A ranar Lahadi Kylian Mbappe da Lionel Messi da kuma Neymar suka buga wa Paris St Germain wasa tare karon farko tun bayan kammala Gasar Kofin Duniya a Qatar.

Argentina ce ta lashe kofin da Messi ya daga, bayan da suka yi nasara a kan Faransa tawagar Mbappe, yayin da Brazil ta Neymar ba ta kai bante ba.

Sun kuma buga wasan Ligue 1 na faransa fafatawar zagaye na 19, inda Rennes ta yi nasara da ci 1-0.

Tun farko an bai wa Messi karin lokacin hutu, domin ya samu damar murnar lashe kofi da suka yi wa kasar na uku jumulla

Sai dai kuma Messi ya ci kwallo da ya koma yiwa PSG tamaula a tsakiyar mako da ta tashi 2-2 da Angers.

Shi kuwa Mbappe bai samu buga wasa biyu ba, bayan da ya je hutu birnin New York tare da abokinsa Achraf Hakimi.

An sa ran za a fara wasa da Mbappe ranar ta Lahadi, sai ya fara da zaman benci daga baya ya canji Hugo Ekitike, inda ya hadu da Messi da Neymar daga gaba.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki