Jaridar Justice watch ta rawaito cewa Alkalan kotun uku da ke jagorantar shari’ar mai shari’a Ngozi Flora ta ce takardun da bangarorin biyu suka gabatar a gaban kotun sun nuna Abdulmumini Jibrin Kofa ya yi murabus daga mukaminsa na babban sakataren hukumar gidaje ta tarayya, kwanaki 30 gabanin gudanar da zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu. 2023 a kan ikirarin mai shigar da kara.
Mai shigar da kara ya gaza na tabbatar da cewa an tafka kura-kurai a Zabe ba tare da bin dokar zabe ta 2022 kamar yadda aka gyara ba.
Don haka an kori karar saboda rashin cancanta.
Kuɗin N100,000 an bayar da shi a haɗin gwiwa da kuma daban-daban akan mai ƙara don goyon bayan waɗanda aka ƙara.
Cikakken labarin zai zo muku nan gaba…..