Jihohin Najeriya na neman Majalisar wakilai ta sa su cikin harkar samar da wuta
Kwamitin ya ɗauki matakin ne bayan da jihohi suka nemi a basu damar shiga harkar a matakai daban-daban, da suka haɗa da samarwa da kuma rarrabawa.
Mahukunta a Najeriya dai sun sha nuna rashin gamsuwa da yadda kamfanonin wutar lantarkin suke gudanar da harkokinsu.
Honourable Magaji Ɗa'u Aliyu, shugaban kwamitin ya shaida wa BBC cewa "akwai kamfanin da ke ruwa da tsaki wajen tafiyar da harkokin wutar lantarki a ƙasar, sai dai ya ce jihohi a yanzu sun nemi a basu dama "su je su yi nasu".
"Mun saurare su, kuma sun kawo mana kundin da suka yi aiki a kai, za mu duba shi sannan kuma za mu faɗa musu halin da ake ciki a kai."
A cewarsa, gaba ɗaya jihohin Najeriya sun sa hannu a takardar da aka miƙa musu "har sun aiko da wakilai daga jihohi guda shida."shida.
Ban da gwamnatocin jihohi, ƙungiyoyi da wasu ɗaiɗaikun jama'a su ma sun bayyana nasu ra'ayin, kuma mafi yawa na nuna goyon baya ga yunƙurin da majalisar ke yi na gyaran fuska ga dokar wutar lantarkin.
Ita ma gwamnatin Najeriya a nata ɓangaren ta ce ta yi na'am da maganar garambawul ɗin sosai sakamakon rashin gamsuwar da ta yi da takun kamfanonin da aka damƙa wa samar da wutar lantarkin a halin da ake ciki.
Minista a ma'aikatar wutar lantarki a Najeriya, Mista Goddy Jedy Agba, ya bayyana cewa yin gyaran na da muhimmanci ga al'ummar ƙasar.
"Muna son gyaran, kowa na son wuta a Najeriya, idan an yi aikin sai mu samu ci gaba."
Ya ce akwai matakai na samar da wutar lantarki - samarwa da rarrabawa kuma a halin da ake ciki, gwamnati kawai tana samar da wutar ne kawai.
"A wannan shekara, za mu cire hannu daga samarwa, zai zama kowa zai taka rawa"
Kwamitin wutar lantarkin dai ya ce zai miƙa bayanan da ya tattara ga zauren majalisar wakilai, kuma a can ne za a yi tankaɗe da rairaya gabanin yanke shawara a kan abin yi.
Batun inganta wutar lantarki daɗaɗɗiyar magana ce a Najeriya, da aka yi yunƙuri daban-daban tun gabanin komawar ƙasar ga dimokraɗiyya, aka kuma ci gaba da kwan-gaba-kwan-baya har zuwa yau.
Kodayake za a iya cewa wutar da ake samarwa ta ƙaru a tsukin nan, amma kuma a ɓangare guda, ƴan ƙasar na kukan cewa ta yi ɗan karen tsada.