Sunayen Unguwannin Da Wike Zai Yi Rusau A Abuja
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya amince a rusa gine-gine sama da 6,000 a yankunan Garki da Jabi da wasu unguwanni 28 da suka saɓa da tsarin birnin tarayyan ba. Hukumar kula da birnin tarayyar (FCTA) ta fitar da jerin sunayen unguwannin, inda ta bayyana cewa gine-ginen ta riga aka sanya wa alama ne rusau din zai shafa, a shirin gwamnati na kawar da gine-ginen da aka yi ba bisa ƙa’ida ba a birnin. Ga jerin unguwannin da abin zai shafa: Apo Mechanic Village Byanzhin. Dawaki. Dai Dai. Durumi. Dutse. Garki. Garki Village. Gishiri. Gwagwalada. Idu. Jabi. Kauyen Kado. Karmo. Karshi. Karu. Katampe. Kauyen Ketti. Kpaduma. Kabusa. Kauyen Kpana. Kubwa. Lokogoma. Lugbe. Mabushi. Mpape. Nyanya. Piya Kasa. Jikwoyi Galadima Tun ranar Litinin da aka rantsar da tsohon gwamnan na jihar Ribas a matsayin Minista, ya sha alwashin dawo da birnin kan ainihin taswirarsa, ruguza gine-ginen aka yi ba bisa tsaru ba, da kuma kawo karshen badaƙalar filaye a babban birnin. Wike wanda ya ce ya zaga birnin...